Ana Matsalar Lantarki, 'Yan Arewa Sun Dura kan Tinubu, Sun Ragargaje Shi

Ana Matsalar Lantarki, 'Yan Arewa Sun Dura kan Tinubu, Sun Ragargaje Shi

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fara shan suka daga wata kungiyar Arewacin Najeriya kan wani mataki da ya dauka
  • A ranar Alhamis shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci ministoci da manyan jami'an gwamnati da su rage ayari da jami'an tsaro
  • Kungiyar League of Northern Democrats ta bayyana dalilin da zai sa dokar da shugaban kasar ya kawo ba za ta yi aiki ba a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya fara shan suka kan umarnin da ya ba ministocin na rage tawaga da jami'an tsaro.

Kungiyar League of Northern Democrats ta ce babu alamar cewa shugaban kasar da gaske yake kan umarnin da ya bayar.

Kara karanta wannan

Raba kasa: Dattijon Arewa, Tanko Yakasai ya hango makomar Najeriya

Bola Tinubu
Kungiyar Arewa ta soki dokar Tinubu ta rage motocin ministoci. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Kakakin kungiyar LND, Ladan Salihu ne ya yi bayani a wata hira da ya yi da gidan Talabijin din Channels a ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar Arewa ta soki Bola Tinubu

Kakakin kungiyar League of Northern Democrats, Ladan Salihu ya ce maganar cewa ministoci su rage tawaga zuwa motoci uku da rage jami'an tsaro ba za ta yiwu ba a kasar nan.

Ladan Salihu ya ce idan da shugaban kasar da gaske yake, shi ya kamata ya fara nunawa ministocinsa rage tawaga da kashe kudin gwamnati.

Kakakin kungiyar ya kara da cewa da na gaba ake gane zurfin ruwa amma Bola Tinubu bai dauki hanyar ba kwata kwata.

Ga abin da yake cewa:

"Babu yadda za a yi ka saye sabon jirgi na Naira biliyan 170 kuma ka saye jirgin zuwa na shakatawa a kan Naira biliyan 5 sannan ka ba ministoci umarnin rage kashe kudi.

Kara karanta wannan

An buƙaci Tinubu ya kara korar ministoci, an kawo sunayen wasu

Idan aka hada kudin da ka kashe a kan jirage kawai ya kusa kai rabin kudin da ministocin za su kashe.
Muna yaudarar kanmu ne kawai idan muka ce wai ministoci za su rage tawaga a Najeriya, hakan ba mai yiwuwa ba ne."

-Salihu Ladan, kakakin LND

Tun bayan sayen sabon jirgin shugaban kasa yan Najeriya suka rika suka kan cewa bai kamata ba lura da halin rayuwa da ake ciki a Najeriya.

An bukaci Tinubu ya kori wasu ministoci

A wani rahoton, kun ji cewa yan Najeriya sun bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kara korar wasu ministocinsa.

Ministan Abuja, Nyesom Ezonwo Wike na cikin jerin ministocin da aka yi kira ga Bola Tinubu ya kora bisa cewa sun gaza tabuka komai tun da aka nada su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng