Awanni bayan Amincewa da Mafi Ƙarancin Albashi, an Shawarci Gwamna da Ya Dakata

Awanni bayan Amincewa da Mafi Ƙarancin Albashi, an Shawarci Gwamna da Ya Dakata

  • An shawarci Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya jinkirta biyan mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan kananan hukumomi
  • Kungiyoyin ma'aikatan kananan hukumomi da na malamai su suka ba gwamnan shawara saboda rashin kammala shirye-shirye
  • Kwamishinan kananan hukumomi da ya jagoranci kungiyoyin Abubakar Garba Dutsinmari ya ce ba a kammala tantance ma'aikatan ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kebbi - Kasa da awa 24 bayan amincewa da mafi ƙarancin albashi, kungiyoyi sun ba gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris shawara.

Kungiyoyin uku sun bukaci Gwamna Nasir Idris ya jinkirta biyan mafi ƙarancin albashi da ya yi niyya.

An bukaci Gwamna ya dakata da biyan mafi ƙarancin albashi
Kwamishina ya shawarci Gwamna Nasir Idris ya jinkirta biyan mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan kananan hukumomi. Hoto: Comrade Nasir Idris.
Asali: Twitter

An ba gwamna shawara kan mafi ƙarancin albashi

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya dakatar da kwamishina saboda kalubantar EFCC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta ce kungiyoyin sun hada da na ma'aikatan kananan hukumomi (NULGE) da na kananan hukumomi (ALGON) da kuma na malamai (NUT).

Shugabannin kungiyar NULGE da ALGON sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a yau Juma'a 25 ga watan Oktoban 2024.

Kwamishinan kananan hukumomi a jihar, Abubakar Garba Dutsinmari ya ce akwai da yawa daga cikin ma'aikatan kananan hukumomi da ba a tantance ba.

Dutsinmari ya ce hakan zai ba da damar kammala tantancewar da kuma sanin yawan ma'aikatan.

"Mu na rokon gwamna da ya daga lokacin biyan mafi ƙarancin albashi wanda ba zai yi kasa da makwanni biyu ba domin kammala shirye-shirye."

- Cewar sanarwar

Albashi: Kungiyoyi sun roki gwamnan Kebbi

Shugaban NULGE, Kwamred Farouk Abubakar Sadiq da ALGON a jihar, Muhammad Nayaya sun roki kwamishinan ya nemi alfarmar gwamnan.

Kara karanta wannan

Damagum: Gwamna a Arewa ya yi amai ya lashe kan shugabancin PDP na ƙasa

Kwamishinan ya ce zai sake komawa wurin gwamnan amma idan hakan bai yiwuwa ba zuwa ranar Litinin dole za a biya kamar yadda ya umarta.

Gwamnan Kebbi zai biya mafi ƙarancin albashi

Kun ji cewa Gwamnan Kebbi, Nasir Idris ya amince zai biya ma'aikatan gwamnatin jihar mafi ƙarancin albashin wanda ya fi N70,000.

Mai girma Gwamna Nasir Idris ya amince zai biya ma'aikatan jihar sabon mafi ƙarancin albashi na N75,000 duk wata.

Gwamnan ya rattaɓa hannu kan dokar sabon mafi ƙarancin albashin ne a gidan gwamnati a ranar Laraba, 23 ga watan Oktoban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.