Gwamnatin Tarayya Ta Amince Gwamna a Arewa Ya Gina Katafaren Filin Jirgin Sama

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Gwamna a Arewa Ya Gina Katafaren Filin Jirgin Sama

  • Gwamnatin jihar Kogi ta mika sakon godiya ga shugaba Bola Tinubu kan amincewa da bukatarta na gina filin jiragen sama
  • Kwamishinan yada labarai na Kogi, Kingsley Fanwo ya ce ma'aikatar sufurin jiragen sama ta amince da bukatarsu na gina filin
  • Mista Kingsley Fanwo ya ce idan aka kammala gina filin jirgin saman a Zariagi zai wadatar da jihohi 10 tare da rage cunkoso a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ma’aikatar sufurin jiragen sama ta tarayya ta amince bukatar gwamnatin jihar Kogi na gina filin jirgin sama na kasa da kasa da kasa a Zariagi.

Kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kogi, Kingsley Fanwo ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a, 25 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Ana fargabar mutane 8 sun mutu a hatsarin jirgin sama, Tinubu ya sa ayi bincike

Gwamnatin jihar Kogi ta yi magana kan samun amincewar gwamnati na gina filin jiragen sama
Gwamnatin Tinubu ta amince jihar Kogi ta gina sabon filin jiragen sama. Hoto: @OfficialOAU
Asali: Twitter

Gwamnati ta amince da bukatar Kogi

Mista Kingsley Fanwo, ya ce ma’aikatar sufurin ta bayar da sanarwar amincewa a wasikar da fitar mai kwanan wata 9 ga Oktoba, 2024, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnatin Usman Ododo ta himmatu wajen ganin an kammala aikin gina filin jiragen saman a kan lokaci tare da bin ka’idojin da aka shimfida.

Kwamishinan ya ce filin jirgin sama na jihar Kogi na da girman da jihohi 10 za su iya amfani da shi wanda zai rage zirga-zirgar ababen hawa a hanyar Lokoja zuwa Abuja.

Amfanin filin jirgin sama a jihar Kogi

Channels TV ta rahoto gwamnatin Kogi ta jaddada cewa filin jirgin da ake shirin ginawa zai rage cunkoso a filin jirgin sama na Abuja.

“Gwamnatin Ododo ta dauki samar da filin jirgin sama na kasa da kasa a matsayin wani babban nauyi da ya rataya kanta da kuma shiga sahun masu harkar sufurin jiragen sama.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan NNPCL sun mutu da jirgin sama ya yi mummunan hatsari, an rasa rayuka

“Wannan aikin zai bunkasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma nunawa duniya irin karfin da jihar take da shi."

- A cewar kwamishinan.

Mista Kingsley Fanwo ya kuma ce gwamnatin jihar Kogi na godiya ga shugaba Bola Tinubu da ministan sufuri bisa amincewa jihar gina wannan filin jirgi.

Gwamna na shan sukar gina filin jirgi

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamantin Zamfara karkashin Dauda Lawal na cigaba da shan kakkausan suka kan kudurin gina filin jirgin sama a jihar.

Gwamna Lawal dai ya dauki aniyar kashe Naira biliyan 62.8 domin gina katafaren filin jirgin sama a Gusau, lamarin da Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya soka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.