Majalisa Ta Yi Adawa da Yi wa Dokar Shari'ar Muslunci Kwaskwarima a Tsarin Mulki
- Majalisar wakilai ta ki amincewa da yi wa sassan da su ka yi magana kan shari'ar Musulunci a kundin tsarin mulki gyara
- Dan Majalisa Aliyu Misau ya bukaci majalisa ta amince a cire kalmar da ke danganta shari'ar ga mutane kawai
- Ya ce kamfanonin Musulunci irinsu bankunan JAIZ da Taj ba za su samu damar Shari'a da su ke bukata ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Majalisar wakilan Najeriya ta yi fatali da ƙudurin da ya nemi a yi wa wasu sassa na kundin tsarin mulkin ƙasa na 1999 kwaskwarima.
Ɗan majalisar PDP, Aliyu Missau ya gabatar da ƙudirin da ke neman a cire wata kalma da ta gabaci shari'ar Muslunci a kundin tsarin mulkin amma takwarorinsa na ganin zai saba tsarin Najeriya.
Jaridar The Cable ta tattara cewa dan majalisar na son a yi gyara ga sashe na 24, 262, 277 da 288 na kundin tsarin mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sashen da ɗan Majalisa ya so a gyara
Jaridar Daily Post ta tattara cewa dan Majalisa ya nemi a cire kalmar 'ƙashin kai' daga sashen da ya jiɓanci shari'ar Musulunci a kundin tsarin mulkin ƙasa
Aliyu Misau ya ce kalmar 'ƙashin kai' da a turance ga zo a 'personal' a dokar ta tauye kamfanonin da ke bin tsarin musulunci irinsu bankin JAIZ da Taj.
Abin da sashen shari'ar Musulunci ya ƙunsa
Sashen da Aliyu Misau ke son a gyara zai tabbatar da kalmar Shari'ar Muslunci ta tsaya da kafarta ba tare da jingina ta da daidaikun mutane ba.
Abin da sashen ya ƙunsha;
"Kotun daukaka kara ta Shari'a, baya ga sauran hukunce-hukuncen da wata doka ta Majalisar Dokoki ta kasa za ta ba ta, za ta yi amfani da irin wannan hukunci da ikon sa ido a cikin shari'o'in da su ka shafi jama'a kan shari'ar Musulunci."
Majalisa na son a daure iyayen yara
A baya kun kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta fara tunanin bijiro da wani ƙuduri da zai ba kotuna damar hukunta iyayen yara marasa zuwa makarantu a fadin ƙasar.
Wannan ya biyo bayan karuwar yara marasa zuwa makaranta da shugaban majalisar Godswill Obot wuya ce yawansu ya kai aƙalla yara miliyan 20.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng