"Jama'a Sun Farga:" Gwamna Ya Hango Karshen Yan Bindiga

"Jama'a Sun Farga:" Gwamna Ya Hango Karshen Yan Bindiga

  • Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana jin dadin yadda jama'a su ka fara kare kansu daga hare haren yan bindiga a kauyuka
  • Mai girma Umaru Dikko Radda ya ce tuni wasu daga cikin yan bindiga su ka fara shiga taitayinsu a maimakon kai hari
  • Gwamnan ya jaddada cewa gwamnati na kan bakarta na taimaka wa mazauna kauyuka wajen dakile harin yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - Gwamnatin Katsina ta bayyana jin dadin yadda jama'a su ka fara daukar shawarwarinta kan yan bindiga da su ka addabe su.

Gwamna Umaru Dikko Radda na daga cikin masu shawartar yan kasar nan su tashi tsaye wajen kare kansu daga harin yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Majalisa na shirin sa a daure iyaye kan rashin tura yara makaranta

Dr Dikko Umaru Radda
Gwamnan Katsina ya ce jama'a sun fara kare kansu daga yan bindiga Hoto: Dr Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

BBC Hausa ta wallafa cewa gwamna Dikko Radda ya ce jama'a sun fara nasara wajen dakile harin da yan ta'adda ke mai masu har gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsaro: Gwamna na alfahari da jama'an Katsina

Gwamna Umaru Dikko Radda ya bayyana cewa mazauna kauyukan jiharsa sun yi nasarar firgita yan bindiga da ke kai masu farmaki.

Ya ce a halin yanzu, akwai kauyukan da yan ta'addan ke fargabar kai farmaki saboda tsauraran matakan kare kai da jama'ar yankunan su ka dauka.

Gwamna ya fadi dabarun dawo da tsaro

Gwamnatin jihar Katsina ta jaddada matsayarta na hada hannu da al'umomin da ke karkara wajen kare rayukansu da dukiyoyinsu.

Dikko Radda da ya bayyana haka ya ce ba a nufin jama'a su dauki makami ba ne bakatatan, sai dai gwamnati za ta horar da matasa domin kare kai.

Gwamnoni sun gana da jagororin tsaro

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnati za ta karbo rancen $600m, a sayo jiragen yaki

A baya mun ruwaito cewa gwamnan Katsina, Umaru Dikko Radda da na Zamfara, Dauda Lawal Dare sun gana da Ministan tsaro na kasa, Muhammad Badaru kan rashin tsaro a jihohinsu.

Haka kuma gwamnonin sun sa labule da Mai ba shugaba Bola Tinubu shawara kan sha'anin tsaro, Nuhu Ribadu kan yadda za a bullowa matsalar yan bindiga a Arewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.