Yan Sanda Sun yi Gumurzu da Yan Bindiga, Sun Ceto Wanda aka Sace

Yan Sanda Sun yi Gumurzu da Yan Bindiga, Sun Ceto Wanda aka Sace

  • Rundunar yan sandan a jihar Katsina ta sanar da cewa ta ceto wani mutum da yan bindiga suka sace a karamar hukumar Jibia
  • Kakakin rundunar yan sanda a jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq ne ya bayyana lamarin ga manema labarai a ranar Alhamis
  • Haka zalika ASP Abubakar Sadiq ya bayyana yadda aka sace mutumin kuma ya shafe sama da wata daya a hannun yan bindigar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Rundunar yan sanda a jihar Katsina ta samu nasara a kan wasu yan bindiga masu garkuwa da mutane.

A wani samame da yan sanda suka kai maboyar yan bindiga, jami'an tsaron sun yi nasarar ceto wani mutum da aka sace.

Kara karanta wannan

'Babba ne sosai,' An fadi wani da haɗarin jirgin NNPCL ya ritsa da shi

Yan sanda
Yan sanda sun ceto matashi a Katsina. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa an sace mutumin ne yayin da yake tafiya a kan babur zuwa wani kauye a Katsina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka sace matashi a jihar Katsina

Kakakin yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa yan bindiga sun sace wani matashi mai suna Mubarak Haruna.

Miyagun sun sace Mubarak Haruna ne a kauyen Kwarare yana tafiya a kan hanyar Katsina zuwa Magamar Jibia.

Yan sanda sun ceto matashi a Katsina

A ranar 24 ga watan Oktoba ne da sassafe yan sanda suka fita wani samame na musamman a karamar hukumar Jibia.

A yayin samamen, yan sanda suka dura kan miyagu yan bindigar a bayan gari kuma suka samu nasarar ceto matashin da suka sace.

An mika matashin da aka sace asibiti

Rundunar yan sanda ta bayyana cewa a yanzu haka ta mika Mubarak Haruna asibiti domin duba lafiyarsa.

Kara karanta wannan

An cafke yan bindiga masu tare hanya suna sace mutane

Bayan haka, rundunar ta tabbatar da cewa yanzu haka ta kara tsananta matakan tsaro domin cafko yan bindigar da ake zargi da sace matashin.

An kama babban dan ta'adda a Kudu

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan yan ta'addan IPOB da ESAN da ke ta'addanci a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

A yayin farmakin da sojojin suka kai, sun yi nasarar cafke wani mugu da ya jagoranci kafa kungiyar ta'addanci ta ESN a Kudu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng