Kotu Ta Yanke Hukunci Kasa da Awanni 24 kafin Zaben Ciyamomi a jihar Kano

Kotu Ta Yanke Hukunci Kasa da Awanni 24 kafin Zaben Ciyamomi a jihar Kano

  • Babbar kotun jiha da ke zamanta a Kano ta yanke hukunci da ya kore hukuncin babbar kotun tarayya kan zaben gobe
  • A baya, babbar kotun tarayya karkashin Simon Amobode ta umarci hukumar KANSIEC ta dakata da gudanar da zabe
  • Amma a hukuncin yau Juma'a, Mai Shari'a Sunusi Ma'aji ya umarci KANSIEC ta yi watsi da wancan umarni, a kuma yi zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - . Babbar kotun Kano ta soke hukuncin babbar kotun tarayya da ta hana gudanar da zaben kananan hukumomi da za a yi a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

"Babu wanda ya isa:" Abba ya yi martani kan hana zaben ƙananan hukumomin Kano

Sabon hukuncin kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Sunusi Ma'aji na zuwa ne kasa da awanni 24 kafin zaben ranar Asabar.

Zaben
Kotu ta sahale a yi zaben Ciyamomi a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

The Guardian ta tattaro Mai Shari'a Ma'aji ya kuma umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tabbata zaben bai samu cikas ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin kotu na soke hana zaben Kano

Mai Shari'a Sunusi Ma'aji ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba wa hukumar zaben iko da alhakin gudanar da zaben kananan hukumomin Kano.

Saboda haka, duk wani yunkuri na hana zaben ya ci karo da dokar kasa, sannan mai Shari'a Sunusi Ma'aji ya umarci hukumar KANSIEC ta gudanar da zabenta.

Zabe: Kotu ta ba yan sanda umarni

Babbar kotun jiha da ke zamanta a Kano ta soke tsohon umarnin kotu da ya hana jami'an tsaro bayar da kariya a rumfunan zaben da za a yi a jihar.

Kara karanta wannan

'Za mu mutunta doka,' ƴan sandan Kano sun dauki matsaya kan shiga zaben ciyamomi

Mai Shari'a Sunusi Ma'aji ya ce wajibi ne yan sanda su fito ranar 26 Oktoba, 2924 domin bayar da tsaro a lokacin gudanar da zaben Ciyamomi.

Gwamna ya yi fatali da hukuncin kotu

A baya kun ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce za su marawa hukumar zabe mai zaman kanta ta a Kano baya domin a tabbata an gudanar da zaben kananan hukumomi.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ba za su zuba idanun wasu tsirarun yan siyasa su nemi hana mutanen Kano gudanar da zaben kananan hukumomi kamar yadda sauran jihohi su ka yi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.