"Haka Ya Shiga Ofis babu Manufa:" Obasanjo Ya Zargi Gwamnatin Tinubu da Aiki da Ka

"Haka Ya Shiga Ofis babu Manufa:" Obasanjo Ya Zargi Gwamnatin Tinubu da Aiki da Ka

  • Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi zargin cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba ta da manufa
  • Ya ce tun farkon fara aiki a matsayin shugaban kasa, Bola Tinubu bai shirya komai don gudanar ayyuka cigaba ba
  • Cif Olusegun Obasanjo na wannan zargi a daidai lokacin da ya ke kokawa da salon magance matsalar tsaron Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ogun - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya caccaki tsarin da Bola Tinubu ke bi wajen gudanar da gwamnati.

Tsohon shugaban kasan ya yi zargin cewa Bola Ahmed Tinubu ba shi da wata sahihiyar hanya ta magance matsalolin da su ka damu Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana matsalar lantarki. 'yan Arewa sun dura kan Tinubu, sun ragargaje shi

Obasanjo
Obasanjo ya caccaki tsarin gwamnatin Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu/@Oolusegun_obj
Asali: Twitter

A wani bidiyon da Theo Abu ya wallafa a shafinsa na X, Cif Obasanjo ya ce da ka Tinubu ya ke mulkin kasar nan ba tare da sanin inda aka dosa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tinubu bai shirya ba:" Obasanjo

Cif Olusegun Obasanjo ya ce yadda Bola Ahmed Tinubu ke gudanar da gwamnati ba za ta haifar da ɗa mai ido wajen magance damuwar ƴan Najeriya ba.

A bidiyon da wata mai amfani da Shafin X, Nafertiti ta wallafa, Obasanjo ya zargi gwamnatin tarayya da wayar gari kawai ta fadi abu ba tare da shiri ba.

Obasanjo ya ba Tinubu misalin mulki na gari

Tsohon shugaban Najeriya a mulkin soja da na farar hula, Cif Olusegun Obasanjo ya ce manufofin da Bola Tinubu ke ayyanawa ba su da inganci.

Ya bayyana cewa a lokacin da ya ke mulkin kasar nan a zamanin soja, gwamnatinsa kan tattauna shiri kafin a bayyana shi ko aiwatar da shi.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya tura sako ga Tinubu awanni bayan raba shi da mukaminsa

Obasanjo ya kadu da rashin tsaro

A baya kun ji cewa tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana damuwa a kan yadda rashin tsaro ke samun gurbin karuwa a sassa daban daban na kasa.

Cif Olusegun Obasanjo ya shawarci Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta daukar matakan da za su kawo karshen matsalolin tsaro da yan Najeriya ke fama da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.