'Za Mu Mutunta Doka,' Ƴan Sandan Kano Sun Dauki Matsaya kan Shiga Zaben Ciyamomi

'Za Mu Mutunta Doka,' Ƴan Sandan Kano Sun Dauki Matsaya kan Shiga Zaben Ciyamomi

  • "Za mu bi umarnin kotu na hana mu shiga zaben kananan hukumomin Kano da ke tafe," a cewar rundunar 'yan sandan jihar
  • Kakakin rundunar 'yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana matsayar rundunar a daren ranar Alhamis
  • Sai dai kuma Abdullahi Kiyawa ya ce rundunar 'yan sandan za ta fito domin tabbatar da tsaro yayin da ake gudanar da zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Rundunar 'yan sanda ta dauki sabuwar matsaya kan ba da tsaro a zaben kananan hukumomin jihar Kano da ke tafe.

Kakakin rundunar 'yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce rundunar ta fasa shiga zaben ciyamomi da na kansilolin jihar mai zuwa.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kasa da awanni 24 kafin zaben Ciyamomi a jihar Kano

Rundunar 'yan sandan Kano ta yi magana kan shiga zaben ciyamomin jihar
Rundunar 'yan sanda ta ce za ta bi umarnin kotu kan shiga zaben ciyamomin Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyaw
Asali: Facebook

'Za mu bi umarnin kotu' - 'Yan sanda

Abdullahi Kiyawa ya bayyana matsayar rundunar 'yan sandan ne a cikin wani sakon faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Jami'an tsaro sun gama shirin bada tsaro da jadawalin jami'an da za a tura a kowacce akwati, na zaben kananan hukumomi mai zuwa, sai ga umarnin kotu kwatsam a kan cewa ka da mu shiga zaben."

- A cewar kakakin 'yan sandan.

Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce biyo bayan wannan umarni na kotu, rundunar ta yanke shawarar mutunta doka, tare da janye shirin shiga zaben.

'Za mu sa ido a zaben' - 'Yan sanda

Sai dai duk da cewa rundunar 'yan sandan ta ce za ta bi umarnin kotu, amma za ta mutunta dokar kasa bisa amfani da sashe na hudu na dokar 'yan sanda ta 2020.

Kara karanta wannan

"Babu wanda ya isa:" Abba ya yi martani kan hana zaben ƙananan hukumomin Kano

"Alhakinmu ne mu tabbatar da cewa ba a samu wadanda suka karya doka da oda a jihar ba. Ba za mu shiga zaben ba amma za mu sanya ido.
"Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Salaman Dogo Garba, ya umarci dukkanin kwamandojojin rundunar da su tabbatar an kare rayuka da dukiyoyin al'umma."

- A cewar Abdullahi Kiyawa.

Kalli bidiyon a kasa:

Kano: Kotu ta hana gudanar da zabe

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya mai zamanta a Kano ta hana gudanar da zaben ciyamomi da na kansilolin jihar Kano.

Mai Shari'a Simon Ameboda wanda ya yanke wannan hukuncin a ranar Talata, 22 ga Oktoba, ya hana jami'an tsaro shiga zaben kananan hukumomin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.