'Yadda 'Yan Ta'adda ke Samun Bindigogi da Harsasan Gwamnati,' Sojoji Sun Yi Bayani
- Rundunar sojin Najeriya ta yi martani ga ikirarin Nuhu Ribadu na cewa jamin tsaro na ba 'yan ta'adda makaman gwamnati
- Daraktan yada labarai na rundunar tsaro, Edward Buba, ya ce babu wani jami'in sojan Najeriya da ke taimakawa 'yan ta'adda
- Buba ya bayyana wasu hanyoyi da 'yan ta'adda ke samun makaman gwamnati ciki har da kai hari sansanin jami'an tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta ce babu wani jami’in soji da ke taimakawa ‘yan bindiga, ‘yan fashi da sauran miyagu da ke addabar kasar nan.
Rundunar ta musanta kalaman da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya yi na cewa sojoji na ba 'yan ta'adda makamai.
'Yan bindiga na satar makaman gwamnati
Rundunar soji ta ce 'yan ta'adda na mallakar makaman gwamnati ne ta hanyar sace su idan suka kai hari kan sansanonin jami’an tsaro inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daraktan yada labarai na tsaro Edward Buba ne ya bayyana hakan a hedikwatar tsaro da ke Abuja, yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis.
Buba ya bayyana cewa rikicin Libiya da rashin zaman lafiya a yankin Sahel ya ba da damar shigo da makamai cikin Najeriya.
Wannan, a cewarsa, ya kara ta’azzara tashe-tashen hankula da ta’addanci a kasar nan.
Yadda makamai ke shiga hannun 'yan ta'adda
Babban jami'in sojan ya ce:
"Idan mu na magana game da yaduwar makamai, da farko dole ne mu dubi abin da ya faru a Libya shekaru da suka wuce da kuma a Sahel.
"Rikicin ne ya ba da damar makamai su shiga hannun mutanen da ba su dace ba, sannan a shigo da su cikin kasarmu, wanda ya kara ta'azzara rashin tsaronmu.
"Na biyu, daga abin da littafi ya ce. Littafi ya ce hanyoyin da 'yan ta'adda ke mallakar makamai sun hada da kai farmaki sansanonin jami'an tsaro da sace makamansu."
Ya ce, duk da haka, rundunar soji ta kan mayar da martani ga irin wannan lamari tare da daukar tsauraran matakai.
An gano masu ba 'yan ta'adda makamai
Tun da fari, mun ruwaito cewa mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya zargi bara-gurbin jami'an tsaron Najeriya da ba yan bindiga makamai.
Nuhu Ribadu ya ce gwamnati ta na sane da wadanda ke kwasar makaman da aka sayo domin yaki da ta'addanci a fadin kasar nan kuma za ta dauki mataki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng