Sarakuna Sun Haɗa Baki, Sun Kai Karar Basarake gaban Gwamna, Sun Roki Alfarma
- Wani basarake ya shiga matsala bayan zarginsa da neman handame wasu filaye a jihar Osun da ke Kudancin Najeriya
- Ogiyan na Ejigbo, Oba Omowonuola Oyeyode ya kai karar Olusongbe na Songbe, Oba Kamilu Ojelabi gaban gwamnan jihar
- Wannan na zuwa ne yayin da gamayyar sarakuna 19 suka bukaci gwamnan ya yi bincike kan matsalar filaye da ake zargin basarake
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Osun - Gamayyar sarakunan gargajiya sun kai korafin dan uwansu wurin Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun.
Sarakunan sun kai karar basarake, Olusongbe na Songbe, Oba Kamilu Ojelabi kan zargin neman cinye wasu filaye.
Sarakuna na zargin basarake da kwace filaye
Punch ta ce Ogiyan na Ejigbo, Oba Omowonuola Oyeyode a madadin sauran sarakunan shi ya kai korafin gaba gwamna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Oba Oyeyode ya bukaci gwamnan da ya kira basaraken da ake zargi domin yi masa tambayoyi kan lamarin.
Ya kuma roki Gwamna Adeleke ya gabatar da binciken a bainar jama'a domin ya zama izina ga wasu da ke shirin yin haka.
"Ya kamata gwamnan ya kira Ojelabi domin yi masa tambayoyi kan abin da ake zarginsa, kuma bayan bincike a wallafa saboda kowa ya gani."
- Oba Omowonuola Oyeyode
Musabbabin zargin basaraken a Osun da ake yi
A cikin sanarwar da sarakunan suka sanyawa hannu, sun zargi basaraken da shiga gonar da ba ta shi ba kan mallakar wasu yankuna a karamar hukumar Ejigbo da ke jihar.
Sarakunan suka ce Olusongbe ya ayyana kansa mamallakin yankuna da dama da suka hada da Idigba da Olorin da Ibogunde da Imoru da Omolosan da kuma Bada da sauran wurare.
Yadda aka fatattaki basaraken a fada
Kun ji cewa Mai Martaba Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya fadi wasu abubuwan da suka faru tsakanin shi da wani sarki.
Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya ce wata rana ya ziyarci fadar Oluwo na Iwo Oba Abdulrasheed Akanbi amma abin bai yi kyau ba.
An ruwaito cewa Oba na Iwo, Abdulrasheed Akanbi ya saba da gardagi ga masu bautar gumaka a Osun da ma kasar Yarabawa.
Asali: Legit.ng