Rai Ya Yi Halinsa: An Shiga Alhini da Tsohon Dan Majalisar Tarayya a Arewa Ya Rasu

Rai Ya Yi Halinsa: An Shiga Alhini da Tsohon Dan Majalisar Tarayya a Arewa Ya Rasu

  • Ana jimamin rasuwar tsohon shugaban hukumar zabe, an sake rashin tsohon dan Majalisar Tarayya daga jihar Kwara
  • Marigayin, Hon. Aliyu Ahman- Pategi shi ne ya wakilci mazabar Edu/ Patigi a jihar Kwara na tsawon shekaru 12
  • An tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne a yau Alhamis 24 ga watan Oktoban 2024 yana da shekaru 59 a duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara - An shiga jimami bayan rasuwar tsohon dan Majalisar Tarayya a jihar Kwara da ke Arewacin Najeriya.

Marigayin Hon. Aliyu Ahman- Pategi ya rasu ne a yau Alhamis 24 ga watan Oktoban 2024 a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan NNPCL sun mutu da jirgin sama ya yi mummunan hatsari, an rasa rayuka

Tsohon dan Majalisar Tarayya a Arewa ya rasu
An shiga alhini kan rasuwar tsohon dan Majalisar Tarayya a Kwara, Hon. Aliyu Ahman- Pategi. Hoto: Aliyu Ahman- Pategi.
Asali: Facebook

Tsohon dan Majalisar Tarayya ya rasu a Kwara

Leadership ta tabbatar cewa marigayin ya rasu ne bayan ya sha fama da jinya yana da shekaru 59 a duniya a yau Alhamis 24 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin ya wakilci mazabar Edu/ Patigi a jihar Kwara inda ya shafe shekaru 12 a Majalisar tarayyar Najeriya da ke birnin Abuja.

Marigayin wanda ya assasa Jami'ar Ahman-Pategi da ke jihar ya rasu kasa da wata biyu cika shekaru 60 a duniya.

Takarar marigayin a kokarin neman gwamna

Har ila yau, Pategi ya yi takara a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a shekarar 2019 karkashin jam'iyyar APC mai mulkin jihar.

Wani abokin harkarsa musamman a harkokin siyasa, Alh Razaq Lawal ya tabbatar da mutuwar marigayin kuma aboki a yau Alhamis 24 ga watan Oktoban 2024.

Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin ya dan bata a ribibin lamuran jihar na wani lokaci kafin rasuwarsa.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban hukumar NEC da ya shirya zaben Abiola 93 ya riga mu gidan gaskiya

Tsohon shugaban hukumar zabe ya bar duniya

Mun ba ku labarin cewa an shiga jimami bayan rasuwar tsohon shugaban hukumar zabe ta Najeriya, Farfesa Humphrey Nwosu a Amurka.

Rahotanni sun tabbatar cewa Farfesa Nwosu ya rasu ne bayan fama da jinya a birnin Virginia da ke kasar Amurka yana da shekaru 83 a duniya.

Shi ya rike muƙamin shugaban hukumar zaɓen daga shekarar 1989 zuwa 1993 lokacin mulkin Ibrahim Badamasi Babangida.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.