Mafi Karancin Albashi: Gwamnan PDP Ya Amince Zai Biya N80,000

Mafi Karancin Albashi: Gwamnan PDP Ya Amince Zai Biya N80,000

  • Ma'aikatan jihar Enugu sun shiga sahun waɗanɗa za a fara biyan mafi ƙarancin albashi a karshen watan Oktoban 2024
  • Gwamna Peter Ndabuisi ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000 a kowane wata ga ma'aikatan jihar Enugu
  • Gwamnan ya bayyana cewa amincewa da sabon mafi ƙarancin albashin na daga cikin alƙawarin da ya ɗauka a lokacin kamfe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Enugu - Gwamnan Enugu, Peter Ndubuisi Mbah ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar.

Gwamna Peter Ndabuisi Mbah ya amince da biyan mafi ƙarancin albashi na N80,000 ga ma’aikatan jihar Enugu, da ke yankin Kudu maso Kudu.

Gwamnan Enugu zai biya albashin N80,000
Gwamna Peter Obi ya amince da sabon albashin N80,000 Hoto: @PNMbah
Asali: Facebook

Gwamnan Enugu ya amince da sabon albashi

Kara karanta wannan

A ƙarshe, Bola Tinubu ya maye gurbin Betta Edu, ya naɗa sabon ministan jin ƙai

Gwamnan ya sanar da amincewa da sabon mafi ƙarancin albashin ne a shafinsa na X a ranar Alhamis, 24 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Mbah ya bayyana cewa za a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin ne daga watan Oktoba.

“Na amince da mafi ƙarancin albashi na N80,000 ga ma’aikatan jihar Enugu, wanda zai fara aiki daga watan Oktoba 2024."
"Muna godiya bisa ƙwazo da sadaukarwar da ma'aikatan jihar suke yi kuma za mu ci gaba da ba da fifiko kan jin daɗin su kamar yadda muka yi alƙawari lokacin yaƙin neman zaɓe."

- Gwamna Peter Ndabuisi Mbah

Amincewar gwamnan na zuwa ne yayin da sauran gwamnoni ke ci gaba da bayyana abin da su riƙa biyan ma'aikata a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.

Gwamna zai biya albashin N80,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Akwa Ibom ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umo Eno ta sanar da biyan mafi ƙarancin albashi na N80,000 ga ma’aikatanta.

Kara karanta wannan

Tinubu na korar ministoci, gwamna ya amince zai biya albashin N80,000

Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Mista Ini Ememobong, ya bayyana cewa biyan N80,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ya nuna cewa gwamnatin ta himmatu wajen kyautata jin daɗin ma’aikata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng