Ana Ta Kiran a Tsige Shi, bayan Ya Sha da Kyar, Minista Ya Yabawa Matakin Tinubu

Ana Ta Kiran a Tsige Shi, bayan Ya Sha da Kyar, Minista Ya Yabawa Matakin Tinubu

  • Ana ta hasashen a za a kore shi, Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya yi magana kan ministocin da aka sallama
  • Ministan ya yabawa matakin da shugaba Bola Tinubu ya dauka na yin garambawul a majalisar ministocinsa
  • Tsohon 'dan takaran gwamnan ya kuma taya sababbin ministocin murnar samun muƙamin da suka yi a gwamnatin Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan makamashi a Najeriya, Adebayo Adelabu ya yi magana kan korar Ministoci da gwamnatin Bola Tinubu ta yi.

Adelabu ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan yin garambawul a gwamnatinsa.

Minista ya yabawa Tinubu kan sallamar Ministoci
Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya yabi Shugaba Bola Tinubu kan matakin garambawul a gwamnatinsa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu Adebayo Adelabu.
Asali: Twitter

Minista ya taya sauran Ministoci murna

Hadimin Ministan a bangaren sadarwa, Bolaji Tunji shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Punch ta samu.

Kara karanta wannan

Dalilin Bola Tinubu na korar ministoci 5 ya bayyana, an faɗi asalin abin da ya faru

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce Adelabu ya taya tsohon Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari, Mr. Sunday Dare murnar samun muƙamin hadimi da Bola Tinubu ya ba shi.

Har ila yau, Adelabu ya kuma taya sauran Ministocin da aka nada mukamai murna inda ya yi musu fatan alheri.

"Nadin da Bola Tinubu ya yi musu ya tabbatar da kwarewarsu da shugabanci nagari da haɗaka da suke da shi."

- Adebayo Adelabu

Minista ya yabawa sabon hadimin Bola Tinubu

Adelabu ya ce nadin tsohon Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari, Mr. Sunday Dare musamman da Tinubu ya yi abin alfahari ne da kuma hanyar kawo sauyi a Najeriya.

Ya ce Dare yana da kwarewa matuka inda ya ce zai yi amfani da dadewa a bangaren yada labarai domin ba kasar gudunmawa mai girma a fannin.

Kara karanta wannan

Awanni bayan Tinubu ya sallame ta, tsohuwar minista ta turawa shi da Remi sako

Matawalle ya tsira daga rasa kujerar Minista

Kun ji cewa karamin ministan tsaro Bello Matawalle na daga cikin mimistocin da garambawul ɗin Tinubu bai shafa ba duk da zargin da ake masa.

Bayo Onanuga ya bayyana cewa zargin da ake yi wa Bello Matawalle kan alaƙa da ƴan bindiga bai da tushe ballantana makama.

Ya nuna cewa binciken da aka yi ya tabbatar da cewa ƙarya ake yi masa wanda hakan ya sa ba a kore shi daga muƙaminsa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.