Matawalle: Dalilin Tinubu Na Barin Minista da Ake Zargi da "Daukar Nauyin 'Yan Bindiga"

Matawalle: Dalilin Tinubu Na Barin Minista da Ake Zargi da "Daukar Nauyin 'Yan Bindiga"

  • Ƙaramin ministan tsaro na daga cikin mimistocin da garambawul ɗin Bola Tinubu bai shafa ba duk da zargin da ake yi masa
  • Bayo Onanuga ya bayyana cewa zargin da ake yi wa Bello Matawalle kan alaƙa da ƴan bindiga bai da tushe ballantana makama
  • Ya nuna cewa binciken da aka yi ya tabbatar da cewa ƙarya ake yi masa wanda hakan ya sa ba a kore shi daga muƙaminsa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hadimin shugaba Bola Tinubu kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana dalilin da ya sa shugaban ƙasan bai kori Bello Matawalle daga muƙaminsa ba.

Hakan na zuwa ne yayin da wasu suka yi tsammanin za a kori ƙaramin ministan tsaron bisa zargin da ake masa na ɗaukar nauyin ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya tura sako ga Tinubu awanni bayan raba shi da mukaminsa

Tinubu bai kori Matawalle a Minista ba
Dalilin Tinubu na kin korar Matawalle Hoto: @DOlusegun, @BelloMatawalle1
Asali: Twitter

A yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Arise Tv a ranar Laraba, Bayo Onanuga ya ce zarge-zargen da ake yi wa Matawalle ba su da tushe ballantana makama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu na da labarin zargin da ke kan Matawalle

Onanuga ya bayyana cewa labaran zargin da ake yi wa Matawalle na ɗaukar nauyin ƴan bindiga a Zamfara sun kai wajen shugaba Bola Tinubu.

Sai dai, ya yi nuni da cewa mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) ya binciki zarge-zargen kuma ya gano cewa ƙarya ne.

Onanuga yake cewa hakan ya sanya Matawalle ya ci gaba da zama a kan muƙaminsa.

Dalilin Tinubu na ƙin korar Matawalle

"Abin da na sani shi ne da yawa daga cikin abubuwan nan zarge-zarge ne kawai. Na taɓa samun ɗaya daga ciki na tura zuwa ga NSA na tambaye shi ko ya san da wannan?"

Kara karanta wannan

Dalilin Bola Tinubu na korar ministoci 5 ya bayyana, an faɗi asalin abin da ya faru

"Ya ce bai da masaniya kuma sun yi bincike kan irin waɗannan zarge-zargen sun gano ba gaskiya ba ne. Mutane kawai suna ƙirƙiro abubuwan ƙarya ne kawai a kan wani mutum."
"Shiyasa har yanzu yake a kan kujerarsa. Hatta shugaban ya ji labarai masu yawa a kansa. Amma zamansa kujerar ya nuna cewa binciken da aka yi kan zarge-zargen ya nuna cewa ƙarya ne."

- Bayo Onanuga

An buƙaci Tinubu ya dakatar da Matawalle

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiya a jam’iyyar APC ta Tinubu Youth Network (TYN), ta bukaci shugaban kasa ya daƙatar da ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle.

Kungiyar ta kuma buƙaci shugaban ƙasan da ya ba da umarnin a gudanar da bincike kan alaƙar Matawalle da ƴan bindiga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng