'Yan Bindiga Sun Kai Hari kusa da Babbar Jami'a, An Rasa Rayuka

'Yan Bindiga Sun Kai Hari kusa da Babbar Jami'a, An Rasa Rayuka

  • Ƴan bindiga da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne sun kai hari a kusa da jami'ar Nnamdi Azikiwe (UNIZIK) da ke jihar Anambra
  • Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an kashe aƙalla mutane shida a harin na safiyar ranar Alhamis, 24 ga watan Oktoban 2024
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin yin abin da ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗ

Jihar Anambra - Wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne sun kai farmaki a Ifite-Awka, kusa da ƙofar jami’ar Nnamdi Azikiwe (UNIZIK) a birnin Awka, jihar Anambra.

Ƴan bindigan a yayin harin sun kashe aƙalla mutane shida har lahira.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da manoma, sun sace kayan abinci

'Yan bindiga sun kai hari a Anambra
'Yan bindiga sun kai farmaki a Anambra Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda ƴan bindiga suka kai hari a Anambra

Wasu shaidun ganau ba jiyau sun shaidawa jaridar The Punch cewa harin ya auku ne da safiyar ranar Alhamis, 24 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun bayyana cewa ƴan bindigan ɗauke da bindigu sun mamaye unguwar ne da sanyin safiyar Alhamis inda suka buɗe wuta kan wasu mutane da ake zargin ƴan wata ƙungiyar asiri ne.

An tattaro cewa ƴan ƙungiyar asirin sun je neman abokan gabarsu ne na wata ƙungiya waɗanda suke harkokinsu a kusa da ƙofar jami'ar UNIZIK.

Sama da mutane shida aka hallaka a kusa da lambun Witness Garden da ke Ifite a kan hanyar Amansea."
"Ƴan daban sun farmaki wajen da misalin ƙarfe 9:30 na safe inda suka fara harbi kan wasu mutane da ake zargin mambobin wata ƙungiyar asiri ce."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka matafiya, sun yi awon gaba da manoma a Neja

- Wani shaida

Ƴan sanda sun yi ƙarin haske

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Legit Hausa.

"Binciken farko ya nuna cewa harsasan ƴan bindigan sun samu mutane uku inda ƴan sanda suka garzaya da su zuwa asibiti.
"An kuma samo kwankwon alburusai a wajen."

- SP Tochukwu Ikenga

Ƴan bindiga sun farmaki ƴan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai hari sansanin ‘yan sandan Mopol da ke Garagi a kauyen Yartsamiyar Jino da ke Katsina.

Rahotanni sun ce ƴan bindigan sun farmaki sansanin 'yan sandan da ke a karamar hukumar Kankara a ranar Talata, 22 ga watan Oktobar 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng