Awanni bayan Tinubu Ya Sallame Ta, Tsohuwar Minista Ta Turawa Shi da Remi Sako
- Tsohuwar Ministar harkokin mata, Uju Kennedy Ohanenye ta yi martani awanni kadan bayan sallamar ta daga mukaminta
- Kennedy Ohanenye ta tura sakon godiya ta musamman ga shugaban kasa, Bola Tinubu game da damar da ya ba ta
- Barista Kennedy ta ce ba za taba mantawa da goyon baya da kuma shawarwarin mai dakinsa, Remi Tinubu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Korarriyar Ministar harkokin mata, Uju Kennedy Ohanenye ta yi magana bayan rasa mukaminta.
Barista Kennedy Ohanenye ta tura sakon godiya ga Bola Tinubu game da damar da ya ba ta a gwamnatinsa.
Tsohuwar Minista ta godewa matar Tinubu
Kennedy Ohanenye ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis 24 ga watan Oktoban 2024 a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohuwar Ministar ta kuma godewa matar shugaban kasa, Remi Tinubu game da goyon bayanta a lokacin da take ofis.
Kennedy Ohanenye ta ce tabbas an ba ta muhimmiyar dama wacce ta yi amfani da ita wurin ba da nata gudunmawa.
Uju ta godewa matar Tinubu, yan Najeriya
"Ina mika sakon godiya ga Shugaba Bola Tinubu kan damar da ya ba ni a gwamnatinsa a matsayin Minista."
"Tabbas abin da ya mani ina alfahari da hakan musamman wurin ba da tawa gudummawar domin kawo cigaban ƙasa."
"Ina kuma godiya ga mai dakin shugaban kasa, Remi Tinubu kan goyon baya da ba da shawarwari."
"Kulawarta da goyon baya shi ne abin ya taimake ni har na samu nasarori a lokacin da nake Minista."
- Uju Kennedy Ohanenye
Uju Kennedy ta kuma godewa yan Najeriya musamman game da goyon baya da suka ba ta lokacin da take ofishin Minista.
Tinubu ya sallami Ministoci 5 a gwamnatinsa
Mun ba ku labarin cewa Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ji kiraye-kirayen al'umma da ya sallami wasu Ministoci biyar.
Shugaban ya dauki matakin ne a ranar Laraba 23 ga watan Oktoban 2024 yayin zaman Majalisar zartarwa da aka yi.
Daga cikin Ministocin da aka kora akwai ta harkokin mata da karamin Ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Gwarzo.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng