Daga Kama Aiki, Sabon Shugaban CCB Zai Tasa Ma'aikatan Gwamnati a Gaba
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar da'ar ma'aikata, Abdullahi Bello a ranar Laraba
- Jim kadan da rantsar da shi, shugaban hukumar ya ce da shirinsa na zo na yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin ma'aikata
- Ya ce daga cikin abubuwan da zai yi a matsayinsa na shugaban CCB, akwai dawo da martabar aikin gwamnatin kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Sabon shugaban hukumar da'ar ma'aikata (CCB), Abdullahi Bello ya sha alwashi kan sabon mukamin da Bola Ahmed Tinubu ya nada shi.
Shugaban kasa, Tinubu ya rantsar da Abdullahi Bello a ranar Laraba yayin gudanar da taron kwamitin zartarwa a Abuja.
Jaridar The Cable ta wallafa cewa sabon shugaban hukumar da'ar ma'aikatan ya ce a shirye ya ke ya dawo da darajar aikin gwamnati a fadin kasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sabon shugaban CCB zai hana rashawa
Sabon shugaban hukumar da'ar ma'aikata, Abdullahi Bello ya ce zai yi kokarin raba ma'aikatan gwamnatin kasar nan da cin hanci da rashawa.
Ya bayyana haka ne jim kadan bayan rantsar da shi, inda ya jaddada akidarsa na dawo da martabar ma'aikatan da aikin gwamnati.
Yadda shugaban CCB zai yaki rashawa
Abdullahi Bello ya bayyana cewa gwamnatin kasar nan za ta iya raba ma'aikatanta da cin hanci da rashawa matukar aka samar da ingantattun tsare-tsare.
Ya ce Najeriya na da shirye-shiryen da za su yaki rashawa, kuma za a yi amfani da su wajen cimma muradin raba ma'aikata da cin hanci.
CCB ta gano matsalar yaki da rashawa
A baya mun ruwaito cewa hukumar da'ar ma'aikatan Najeriya ta ce ta gano dalilin da ya sa ake samun rashin nasara wajen yaki da cin hanci da rashawa a fadin kasar nan.
Shugaban hukumar na wancan lokaci, Barista Murtala Kankia ya ce matsaloli biyu da ke ci masu tuwo a kwarya su ne rashin isassun kudi da karancin ma'aikatan da za su yaki rashawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng