Gwamna a Arewa Ya Dakatar da Kwamishina saboda Kalubantar EFCC
- Gwamnan jihar Benue, Alia Hyacinth ya dakatar da wani kwamishinansa kan shiga shari'a ba tare da saninsa ba
- Alia ya dauki matakin ne kan kwamishinan shari'a, Fidelis Mynin game da korafin da ake yi kan hukumar EFCC
- Hakan ya biyo bayan maka hukumar EFCC da aka yi a kotu kan rashin ingancin dokar da ta samar da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Benue - Gwamna Alia Hyacinth na Benue ya dakatar da kwamishinan shari'a a jihar, Fidelis Mynin.
Alia ya dauki wannan mataki ne bayan kwamishinan ya shiga korafi kan dokar da ta samar da hukumar EFCC a kasar.
Yadda gwamnoni suka maka EFCC a kotu
Kakakin gwamnan, Kula Tersoo shi ya tabbatar da haka ga jaridar Punch a yau Laraba 23 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan shigar da korafi a Kotun Koli da wasu jihohi 16 suka yi a Najeriya kan dokar da samar da hukumar EFCC.
Tun farko jihar Kogi ce ta fara shigar da korafi sannan jihohi 15 suka mara mata baya kafin gwamnatin Anambra ta janye daga cikin lamarin.
Karar EFCC: Gwamna ya dakatar da kwamishinansa
Alia ya dakatar da kwamishinan ne saboda shiga shari'ar da ya yi ba tare da neman sahalewarsa ba wanda ya ji zafin sosai, cewar rahoton TheCable.
Tersoo a cikin sanarwar ya tabbatar da cewa Gwamna Alia ya dauki matakin saboda shiga shari'ar da aka yi babu izninsa.
"Tabbas, da gaske ne, Gwamna Alia ya dakatar da kwamishinan shari'a saboda kalubalantar dokar da ta kafa EFCC babu izininsa."
- Kula Tersoo
An maka Gwamna Alia Hyacinth a kotu
Kun ji cewa Gwamnan jihar Benue a Arewacin Najeriya ya shiga matsala bayan dan Majalisar Tarayya daga jiharsa ya maka shi a kotu.
Dan Majalisar Tarayya, Terseer Ugbor ya maka Gwamna Alia Hyacinth da mukarrabansa biyu kan zargin bata masa suna.
Hon. Ugbor ya shigar da korafin a babbar kotun jihar da ke birnin Makurdi a jihar Benue a ranar Juma'a 11 ga watan Oktoban 2024.
Asali: Legit.ng