Gwamna Abba Kabir Ya Nada Ahmed Musa Mukami a Gwamnatinsa
- Gwamnatin jihar Kano ta ba kyaftin ɗin tawagar ƴan wasan Super Eagles, Ahmed Musa muƙami
- Mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Ahmed Musa a muƙamin jakadan wasanni na jihar Kano
- Ɗan wasan ƙungiyar Kano Pillars ya miƙa saƙon godiyarsa ga gwamnatin bisa wannan naɗin da ta yi masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ba Ahmed Musa muƙami.
Gwamna Abba Kabir ya naɗa kyaftin ɗin na Super Eagles a matsayin jakadan wasanni na jihar Kano.
Ahmed Musa ya sanya takardar naɗin a shafinsa na X mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi a ranar Laraba, 23 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, sakataren gwamnatin na Kano ya tabbatar da cewa naɗin zai fara aiki ne daga ranar, 24 ga watan Yulin 2024.
"Ina matuƙar farin farin ciki sanar da kai cewa mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da naɗin ka a matsayin jakadan wasanni na jihar Kano daga ranar 24 ga watan Yuli, 2024."
- Abdullahi Baffa Bichi
Ahmed Musa ya yi godiya
Kyaftin ɗin na Super Eagles ya miƙa saƙon godiyarsa kan wannan naɗin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi masa.
"Ina matuƙar farin ciki da aka naɗa ni jakadan wasanni na jihar Kano!"
"Ina godiya ga gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan gagarumin nauyi.
"A tare za mu zaburar da matasa masu tasowa don cimma nasarori a ciki da wajen fili. Mu zo mu kafa tarihi!"
- Ahmed Musa
An naɗa Ahmed Musa sarauta
A wani labarin kuma, kun ji cewa shahararren ɗan wasan Najeriya, Ahmed Musa ya samu sarautar gargajiya ta 'Shetiman Kwallon Kafar Nguru' ranar Lahadi, 9 ga watan Yunin 2024.
Sarkin Nguru, Alhaji Mustapha Ibn Mai Kyari ne ya naɗa keftin din tawagar Super Eagles wannan saurata bayan wata ziyara da ya kai fadarsa da ke Nguru, jihar Yobe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng