'Ba Mu Yarda ba': Wani Dattijo Ya Nuna Tinubu da Yatsa kan Rusa Ma'aikatar Neja Delta

'Ba Mu Yarda ba': Wani Dattijo Ya Nuna Tinubu da Yatsa kan Rusa Ma'aikatar Neja Delta

  • Wani jagoran Kudu maso Kudu, Cif Edwin Clark ya ce al'ummar shiyyarsa ba za su amince da rusa ma'aikatar Neja Delta ba
  • Ma'aikatar bunkasa Neja Delta na daga cikin ma'aikatun da shugaba Bola Tinubu ya rusa a yayin yiwa gwamnati garambawul
  • Cif Edwin Clark ya zargi shugaba Tinubu da rusa ma'aikatar domin yin amfani da kudin shiyyar wajen raya sauran shiyyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon kwamishinan yada labarai na tarayya Cif Edwin Clark ya yi martani ga sauye sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya yi a ma'aikatun kasar nan.

Edwin Clark, wanda kuma kuma jagoran Kudu-maso-Kudu ne ya ce al'ummar yankinsa ba za su amince Tinubu ya rusa ma'aikatar Neja Delta ba.

Kara karanta wannan

Bayan korar ministoci, Tinubu ya rantsar da dan Arewa a babban muƙami

Edwin Clerk ya yiwa Tinubu martani kan rusa ma'aikatar raya Neja Delta
Edwin Clerk ya ce ba Kudu maso Gabas ba za su amince da rusa ma'aikatar Neja Delta ba. Hoto: @IU_Wakilii
Asali: Twitter

Dattijo a Kudu ya caccaki Shugaba Tinubu

A martaninsa game da rusa ma'aikatar harkokin Neja Delta, dattijon ya bayyana cewa babu shugaban kasar ba shi da wani dalili na yin hakan, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cif Clark ya zargi gwamnatin Tinubu da shirin yin amfani da kudin da ake samu daga Kudu-maso-Kudu wajen bunkasa ma'aikatun sauran shiyyoyin kasar da aka kafa.

A cewar shugaban kungiyar Pan Niger Delta (PANDEF), Shugaba Tinubu ba shi da wani kyakkyawan shiri ga ci gaban al'ummar Neja.

Jigo ya soki rusa ma'aikatar Neja Delta

Ya ce marigayi shugaba Umaru Yar’Adua ya kirkiro ma’aikatar ne domin ci gaban yankin da tabbatar da zaman lafiya na dindindin da kuma magance matsalar satar mai.

Cif Clark wanda kuma shi ne jagoran kungiyar shugabannin Kudu da Arewa ta tsakiya ya ce:

"Babu dalilin soke ma'aikatar a yanzu, Yar’adua yana da dalilin samar da ita, domin bunkasa yankin Neja-Delta da Nijeriya, domin samar da zaman lafiya a yankin.

Kara karanta wannan

Ministoci: Tinubu ya nada matar Ojukwu da Ministan Buhari da wasu mutane 5

"Ba za mu yarda a rusa ta ba, gwamnati na son amfani da kudin Kudu maso Kudu wajen bunkasa sauran hukumomin raya shiyyoyin kasar nan."

Garambawul: Tinubu ya rusa ma'aikatu

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta amince da rushe ma'aikatun wasanni da kuma ta Neja Delta a yankin Kudu maso Kudancin Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta cimma wannan matsayar ne a zaman majalisar zartarwa da Bola Tinubu ya jagoranta a ranar Laraba, 23 ga Oktoba, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.