Tinubu Na Korar Ministoci, Gwamna Ya Amince Zai Biya Albashin N80,000
- Gwamnatin Akwa Ibom ta sanar da mafi ƙarancin albashin da za ta biya ma'aikatan jihar da ke yankin Kudu maso Kudu
- Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Umo Eno ta sanar da cewa za ta biya ma'aikatan jihar sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000 a wata
- Kwamishinan labaran jihar ya sanar da hakan inda ya ƙara da cewa an kafa kwamitin da zai tabbatar da an aiwatar da ƙarin albashin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Akwa Ibom - Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta sanar da biyan mafi ƙarancin albashi na N80,000 ga ma’aikatanta.
Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Mista Ini Ememobong, ya bayyana cewa biyan N80,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ya nuna cewa gwamnatin ta himmatu wajen kyautata jin daɗin ma’aikata.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ini Enemobong ya sanyawa hannu ranar Laraba a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Uno zai biya albashin N80,000
Ememobong ya bayyana cewa Gwamna Umo Eno ya kafa kwamitin da zai tabbatar da aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
"Gwamnan Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta biya sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000 ga ɗaukacin ma’aikatan jihar."
"Domin tabbatar da gudanar da wannan tsarin, gwamnan ya kuma kafa kwamitin aiwatarwa, wanda aka ba shi wata ɗaya ya gabatar da rahotonsa kan yadda za a yi ƙarin albashin."
- Ini Ememobong
Kwamitin mai mambobi 15 da shugaban ma’aikatan gwamnati, Elder Effiong Essien ke jagoranta ya ƙunshi shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC.
Akwai 'yan ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta Najeriya (NULGE) da sauransu.
Karanta wasu labaran kan mafi ƙarancin albashi
- Gwamna Ya kere tsara, ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi sama da N80,000
- Gwamnan APC ya ciri tuta, ya sanar da sabon albashin da zai fara biyan ma'aikata
- Gwamnan PDP ya umarci biyan mafi ƙarancin albashin N70,000 nan take
Gwamna zai biya albashin N75,000
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da biyan sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata.
Gwamna Nasir Idris ya amince da N75,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan gwamnatin jihar da ke yankin Arewa maso Yamma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng