Ministoci: Tinubu ya Nada Matar Ojukwu da Ministan Buhari da Wasu 5

Ministoci: Tinubu ya Nada Matar Ojukwu da Ministan Buhari da Wasu 5

  • Shugaba Bola Tinubu ya nada sababbin Ministoci guda bakwai bayan sallamar wasu daga ciki da kuma yin sauye-sauye
  • Tinubu ya amince da nadin matar marigayi Odumegu Ojukwu da ake kira Bianca Odinaka Odumegu-Ojukwu a matsayin karamar Minista
  • Shugaban ya kuma amince da nadin tsohon Ministan Buhari, Muhammadu Maigari Dingyadi a matsayin Ministan ayyuka da kwadago

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jim kadan bayan sallamar wasu Ministoci da sauye-sauye a gwamnatinsa, Bola Tinubu ya nada sababbi.

Tinubu ya amince da nadin Bianca Odinaka Odumegu-Ojukuwu a matsayin ƙaramar Ministar harkokin waje.

Tinubu ya nada sababbin Ministoci bayan sallamar wasu
Bola Tinubu ya nada Ministan Buhari da wasu mutum 5 a muƙamin Ministoci. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Sababbin Ministoci da Tinubu ya nada

Hadimin shugaban a bangaren sadarwa, Dada Olusegun shi ya tabbatar da haka a shafinsa na X a yau Laraba 23 ga watan Oktoban 2024.

Kara karanta wannan

A karshe, Tinubu ya ji korafe korafen yan Najeriya, ya sallami Ministoci 5

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan Tinubu ya yi garambawul a ma'aikatun gwamnati inda ya rushe ma'aikatun wasanni da kuma na Neja Delta.

Tinubu ya kuma hade ma'aikatar yawon bude ido da na al'adu da bunkasa tattalin arziki da Hannatu Musa Musawa ke jagoranta.

Daukar matakin ya zo a daidai lokacin da ake ta korafi kan wasu Ministoci da ba su tabuka wani abun a zo a gani ba a cikin shekara daya.

Sauran sababbin Ministocin sun hada da:

Sauran wadanda suka samu mukaman Ministocin akwai Dakta Nentawe Yilwatda a matsayin Ministan jin kai da walwala da Muhammadu Maigari Dingyadi a ma'aikatar ayyuka da kwadago.

Sai kuma Dakta Jumoke Oduwole a ma'aikatar kasuwanci da zuba hannun jari da Idi Mukhtar Maiha a ma'aikatar cigaban kiwon dabbobi.

A cikin sababbin akwai Hon. Yusuf Abdullahi Ata muƙamin karamin Ministan gidaje da raya birane sai kuma Suwaiba Said Ahmad, PhD a muƙamin karamar Ministar ilimi.

Kara karanta wannan

Ana dakon korar Ministoci, Tinubu ya rushe ma'aikatu, ya yi garambawul a gwamnati

Tinubu ya kori Ministoci 5 a gwamnatinsa

A baya, mun baku labarin cewa Shugaba Bola Tinubu ya ji korafe-korafen al'umma inda ya kori wasu daga cikin Ministocinsa.

Shugaban ya dauki matakin ne a yau Laraba 23 ga watan Oktoban 2024 yayin zaman Majalisar zartarwa da aka yi.

Daga cikin Ministocin da aka kora akwai ta harkokin mata da karamin Ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Gwarzo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.