A Karshe, Tinubu Ya Ji Korafe Korafen Yan Najeriya, Ya Sallami Ministoci 5
- Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ji kiraye-kirayen al'umma da ya sallami wasu Ministoci guda biyar
- Shugaban ya dauki matakin ne a yau Laraba 23 ga watan Oktoban 2024 yayin zaman Majalisar zartarwa da aka yi
- Daga cikin Ministocin da aka kora akwai ta harkokin mata da karamin Ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Gwarzo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya sallami wasu Ministoci guda biyar a gwamnatinsa.
Bola Tinubu ya dauki wannan mataki ne bayan kiraye-kiraye da yan kasar ke yi masa na ya sallami wasu daga ministoci.
Jerin Ministoci da Bola Tinubu ya sallama
Channels TV ta tabbatar da cewa Bola Tinubu ya sallami Ministocin ne a yau Laraba 23 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin wadanda abin shafa akwai Ministar harkokin mata, Uju-Ken Ohanenye da Ministan yawon buɗe ido, Lola Ade-John, cewar Punch.
Sauran sun hada Ministan ilimi, Tahir Mamman da Abdullahi Gwarzo wanda ke riƙe da mukamin karamin Ministan gidaje da raya birane da kuma Ministar matasa, Jamila Ibrahim.
Sauyi a ma'aikatar wasanni
Har ila yau, bayan rusa ma'aikatar harkokin wasanni, Tinubu ya nada Shehu Dikko a matsayin shugaban hukumar wasanni (NSC).
Dikko shi zai jagoranci maiakatar bayan sallamar Ministanta, Sanata John Enoh domin kawo sauyi a harkokin wasanni.
Karanta wasu labaran kan Ministoci a Najeriya
Ana Dakon Korar Ministoci, Tinubu Ya Rushe Ma'aikatu, Ya Yi Garambawul a Gwamnati
Ministoci Sun Firgita da Dawowar Tinubu, An Fadi Lokacin da Ake Ganin Zai Kori Wasu
Shugaba Tinubu Ya Aika Muhimmin Saƙo Ga Ministoci 5 da Ya Kora Daga Aiki
Tinubu ya nada sababbin Ministoci a gwamnatinsa
Kun ji cewa jim kadan bayan sallamar wasu Ministoci da sauye-sauye a gwamnatinsa, Bola Tinubu ya nada sababbi.
Tinubu ya amince da nadin Bianca Odinaka Odumegu-Ojukuwu a matsayin ƙaramar Ministar harkokin waje.
Sauran sun hada Dakta Nentawe Yilwatda a matsayin Ministan jin kai da walwala da Muhammadu Maigari Dingyadi a ma'aikatar ayyuka da kwadago.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng