Mafi Karancin Albashi: Gwamnan Jihar Arewa Ya Amince Zai Biya N75,000
- Gwamnan Kebbi, Nasir Idris ya amince zai biya ma'aikatan gwamnatin jihar mafi ƙarancin albashin wanda ya fi N70,000
- Mai girma Gwamna Nasir Idris ya amince zai biya ma'aikatan jihar sabon mafi ƙarancin albashi na N75,000 duk wata
- Gwamnan ya rattaɓa hannu kan dokar sabon mafi ƙarancin albashin ne a gidan gwamnati a ranar Laraba, 23 ga watan Oktoban 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da biyan sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata.
Gwamna Nasir Idris ya amince da N75,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan gwamnatin jihar da ke yankin Arewa maso Yamma.
Gwamnan Kebbi zai biya N75,000
Gwamna Nasir Idris ya rattaɓa hannu a kan dokar mafi ƙarancin albashin ma’aikata a ranar Laraba, 23 ga watan Oktoban, wata sanarwa a shafin X na gwamnatin jihar ta tabbatar da hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya sanya hannu kan dokar ne a yayin wani taro a gidan gwamnatin jihar wanda ya samu halartar jami'an ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), ƙarƙashin jagorancin, Joe Ajaero.
Tun da farko dai gwamnan ya taka rawar gani wajen ganin an aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi.
A lokacin da akasarin gwamnonin jihohin Najeriya suka ce ba za su iya biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba, gwamnan tsaya tsayin daka kan cewa gwamnoni za su iya biyan sabon albashin.
Gwamna Nasir ya yi ƙoƙari
Lukman Isah Kamba ya shaidawa Legit Hausa cewa tabbas gwamnan ya yi ƙoƙari bisa amincewa da sabon mafi ƙarancin albashin.
"Mu a jihar Kebbi sai san barka domin Gwamna Nasir yana ƙoƙari sosai. Kuma wannan kuɗin da ya amince da su za su taimaka sosai ga ma'aikata."
- Lukman Isah Kamba
Karanta wasu labaran kan mafi ƙarancin albashi
- Mafi karancin albashi: Ana murna, gwamna ya sanar da lokacin fara biyan N70,000
- Daga karshe, Abba ya magantu kan karin albashi, ya yi wa ma'aikatan Kano albishir
- Mafi karancin albashi: Jerin gwamnonin da za su biya ma'aikata fiye da N70000
Gwamna ya amince zai biya N85,000
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara ya amince da N85,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a jihar da ke yankin Ƙudu maso Kudu na Najeriya.
Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Rivers, George Nwaeke, shi ne ya sanar da haka a ranar Jumua'a, 18 ga watan Oktoba, 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng