Tsohon Gwamna Ya Yi Fallasa, Ya Fadi Abin da Ke Firgita Gwamnoni a Mulki
- Tsohon gwamnan jihar Ogun, Olusegun Osoba ya bayyana cewa akwai rashin yarda tsakanin shugabanni da mataimakansu
- Ya bayyana haka ne a taron tsofaffin mataimakan gwamnoni a kasar nan da ya gudana karo a uku a babban birnin tarayya Abuja
- Osoba ya ce ba a kasar nan ko nahiyar Afrika kawai ake samun matsalar ba, ana samun irin wannan a dukkanin sassan duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Ogun - Tsohon gwamnan jihar Ogun, Olusegun Osoba ya fadi abin da ke ba gwamnoni da shugabannin kasashe tsoro game da mataimakansu.
Tsohon gwamnan ya ce shugaban kasa da gwamnoni na fargabar mika mulki ga mataimakansu, kuma akwai dalilai masu karfi a kan haka da su ka hada da tsoron makarkashiya.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Olusegun Osaba, wanda tsohon dan jarida ne ya bayyana haka a taron shekara-shekara na kungiyar tsofaffin mataimaka gwamnoni karo na uku a Abuja.
Tsohon gwamna ya fadi fargabar gwamnoni
Tsohon gwamnan Ogun, Olusegun Osaba ya shaidawa taron tsofaffin mataimaka gwamnoni a Abuja cewa babu yarda da aminci a tsakanin gwamnani da mataimakansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa haka kuma akwai rashin yarda a tsakanin shugabannin kasashe da mataimakansu, shi ya sa ba sa son mika masu ragamar mulki ko da na wucin gadi ne.
Tsohon gwamna ya yi bayanin matsalar mulki
Tsohon gwamna Olusegun Osoba ya bayyana cewa matsalar rashin aminci tsakanin shugabanni da mataimakansu ba a Najeriya ko nahiyar Afrika kawai ake samun shi ba.
Ya bayyana cewa wannan ta sa ake yawan ganin gwamnoni na bi ta karkashin kasa, su na neman a tsige mataimakansu a manyan kasashen duniya kamar Amurka.
Tsohon gwamnan ya ce wannan matsala ce babba, kuma ta na haddasa zaman doya da manja da rashin fuskantar juna tsakanin jagororin jama'a a fadin duniya.
Gwamna ya fadi matsayin mataimakinsa
A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Edo ta ki amincewa da hukuncin babbar kotu da ke zamanta a jihar na dawo da korarren mataimakin gwamna, Philip Shaibu mukaminsa.
Kwamishinan yada labaran jihar, Chris Osa ya ce gwamnati ba ta amince da hukuncin babbar kotun ba, kuma za ta daukaka kara, saboda haka Philip Shaibu korarre ne a idonta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng