Ana Dakon Korar Ministoci, Tinubu Ya Rushe Ma'aikatu, Ya Yi Garambawul a Gwamnati
- A yau Laraba 23 ga watan Oktoban 2024, shugaban kasa ya rushe wasu daga cikin ma'aikatun tarayya a Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu shi ya jagoranci zaman majalisar inda suka rusa ma'aikatun Neja Delta da na harkar wasanni
- Hakan na zuwa ne yayin da ake ta rade-radin shugaba Tinubu zai sallami wasu daga cikin Ministoci a makon nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya jagoranci zaman majalisar zartarwa da aka yi a birnin Tarayya Abuja.
Yayin zaman, Tinubu da majalisar sun amince da rushe wasu daga cikin ma'aikatu da Ministoci ke jagoranta.
Tinubu ya rushe wasu ma'aikatu a gwamnatinsa
Hadimin shugaban a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga shi ya tabbatar da haka a shafinsa na X a yau Laraba 23 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Onanuga ya ce majalisar ta amince da rushe ma'aikatun wasanni da kuma na Neja Delta a yankin Kudu maso Kudancin Najeriya.
Gwamnatin Tinubu ta kawo sabuwar ma'aikata
A yanzu za a samar da ma'aikatar cigaban yankuna da za ta kula da Hukumar raya yankin Arewa ta Gabas da kuma Yamma.
Sai kuma hukumomin raya yankunan Kudu maso Yamma da Neja Delta da aka kirkira domin cigaban yankunansu.
Wasu sauye-sauye da Bola Tinubu ya kaddamar a yau
Hukumar wasanni ta kasa ita za ta dawo ma'aikatar wasanni da a baya ke karkarshin jagorancin ministanta, John Owan Enoh.
Har ila yau, Tinubu ya hade ma'aikatar yawon bude ido da kuma ta al'adu da fikirar tattalin arziki da ke karkashin jagorancin Hannatu Musa Musawa.
Dukan wadannan matakai an tabbatar da su ne yayin zaman majalisar zartarwa na farko tun bayan dawowar Bola Tinubu daga Faransa.
Ana hasashen Tinubu zai sallami wasu Ministoci
Kun ji cewa wasu rahotanni sun tabbatar da cewa akwai yiwuwar Bola Tinubu ya sallami wasu daga cikin Ministoci.
Tun bayan dawowarsa a karshen mako, ake hasashen komai zai iya faruwa da wasu Ministoci da masu rike da mukamai.
Hakan bai rasa nasaba da doguwar ganawa da Tinubu ya yi da hadimarsa a bangaren kula da kokarin masu muƙamai, Hadiza Bala Usman.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng