Sarkin Musulmi, Gwamnonin Arewa Sun Halarci Taron Samar da Tsaro a Aso Villa

Sarkin Musulmi, Gwamnonin Arewa Sun Halarci Taron Samar da Tsaro a Aso Villa

  • Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya halarci wani taro a fadar shugaban kasa domin inganta tsaron yanar gizo
  • An ruwaito cewa matar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu da wasu gwamnonin Arewa na cikin waɗanda suka halarci muhimmin taron
  • Hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ce ta shirya taron domin yaki da barnar da ake yi ta yanar gizo a kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta shirya taron samar da tsaron yanar gizo a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

'Ya ƙware': Yadda ɗan shekara 17 ya yi kutse a na'urar shugaban hukumar EFCC

Taron ya samu halartar manyan mutane daga sassan Najeriya ciki har da mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III.

Sarkin Musulmi
An yi taro kan tsaro a Aso Villa. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad.
Asali: Facebook

Hadimin gwamna Dikko Radda, Ibrahim Kaulaha Muhammad ne ya wallafa yadda taron ya gudana a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi taron tsaron yanar gizo a Abuja

Hukumar EFCC ta shirya taro na musamman domin yaki da sata da damfara a kafafen yanar gizo a Najeriya.

Taron ya mayar da hankali kan yadda za a rika amfani da basira wajen samar da hanyoyin cigaba a yanar gizo maimakon sata da damfara.

Manyan baki da suka halarci taron

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar na cikin waɗanda suka halarci taron a fadar shugaban kasa.

Haka zalika matar shugaban kasa, ministan matasa, matar gwamnan Kwara da shugaban hukumar NITDA na cikin waɗanda suka je.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi barazanar sauke sarakuna saboda rashin tsaro

Oluremi Tinubu ce ta bude taron kuma ta yi kira kan amfani da fasahar zamani wajen gina kasa.

Gwamnonin Arewa da suke je taron tsaro

Shugaban gwamnonin Arewa, Muhammad Inuwa Yahaya da gwamnan Katsina sun halarci taron.

Gwamnonin Kwara da Zamfara sun je, suka nuna muhimmacin samar da tsaron yanar gizo domin cigaban Najeriya.

Kotu za ta yi hukunci tsakanin EFCC da jihohi

A wani rahoton, kun ji cewa kotun Koli ta tanadi hukunci kan ƙarar da gwamnoni 16 suka shigar inda suke ƙalubalantar dokar da ta kafa EFCC.

Kotun mai alƙalai bakwai ta tanadi hukunci ne kan ƙarar yayin zamanta na ranar Talata, 22 ga watan Oktoban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng