Majalisar Tarayya Ta Shirya Kirkiro Karin Jiha 1 a Najeriya, Bayanai Sun Fito

Majalisar Tarayya Ta Shirya Kirkiro Karin Jiha 1 a Najeriya, Bayanai Sun Fito

  • Majalisar wakilai ta fara yunkurin kirkiro sabuwar jiha a Najeriya inda take shirin raba Oyo zuwa jihohi biyu, kamar Ibadan da Oyo
  • Akeem Adeyemi da wasu ‘yan majalisu ne suka dauki nauyin kudirin, sun nemi a kafa jihar Ibadan, da Ibadan a matsayin babban birni
  • Matakin dai na daga cikin gyaran kundin tsarin mulkin da ake yi, kuma irinsa na biyu na neman karin jihohi a Kudu maso Yammaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar tarayya ta fara shirye shiryen raba jihar Oyo zuwa gida biyu, inda za a kirkiro sabuwar jiha daga Oyon.

Kudirin dokar da dan marigayi Alaafin na Oyo, Akeem Adeyemi, da ‘yan majalisar tarayya shida a suka dauki nauyi ya tsallake karatu na biyu.

Kara karanta wannan

Yadda aka cafke Bobrisky da tsakar dare yana shirin guduwa daga Najeriya

Majalisar wakilai ta fara shirin raba jihar Oyo gida biyu.
Kudurin dokar raba jihar Oyo gida biyu ya tsallake karatu na biyu a majalisar dokokin kasar. Hoto: @LegendaryJoe
Asali: Twitter

Majalisa ta shirya raba jihar Oyo

Premium Times ta ruwaito cewa kudirin dokar ya tsallake karatu na biyu ba tare da muhawara ba, yayin da kakakin majalisar Abbas Tajudeen ya bayyana shi a matsayin "madaidaici."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ci gaban dai ba shi ne karon farko na yunkurin raba jihar Oyo ba, domin a baya an gabatar da kudirin dokar kafa jihohin Oke-Ogun da Ibadan amma suka gaza tsallakewa.

Wani abin sha’awa kuma shi ne, a halin yanzu ana kan duba wani kudirin doka da Oluwole Oke ya dauki nauyinsa, inda ya bada shawarar kafa jihar Oke-Ogun.

Kafuwar Oyo da neman raba ta

An fara kafa Jihar Oyo ne daga tsohuwar Jihar Yamma a ranar 3 ga Fabrairu, 1976, a lokacin mulkin Janar Murtala Mohammed na mulkin soja, inji rahoton WikiPedia.

A baya dai an samu sauye-sauye a jihar, inda a shekarar 1991 aka raba ta da jihar Osun. Daular Oyo daular Yarbawa ce mai karfi da ta yi mulki a yankin daga c. 1300 zuwa 1896.

Kara karanta wannan

Ana kukan lantarki, ruwa ya karya gadar da ta haɗa ƙauyuka sama da 50

The Cable ta rahoto cewa an mika kudirin dokar raba jihar Oyo ga kwamitin duba kundin tsarin mulki domin kara daukar matakin aiwatar da shi.

An gabatar da kudurin kafa jihar Etiti

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa wasu 'yan majalisa biyar sun gabatar da kudirin neman kirkiro jihar Etiti kuma har an masa karatu na farko.

Kudirin ya buƙaci a fitar da sabuwar jihar daga jihohi biyar na Kudu maso Gabas, Abia, Enugu, Anambra, Ebonyi da Imo wanda hakan zai karawa yankin jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.