Sankara: Kotu Ta ba 'Yan Sanda Umarni kan Kwamishinan Jigawa da Aka Dakatar

Sankara: Kotu Ta ba 'Yan Sanda Umarni kan Kwamishinan Jigawa da Aka Dakatar

  • Wata kotun shari'ar musulunci da ke Kano ta umarci ƴan sanda su yi bincike kan zargin lalata da ake yi wa dakataccen kwamishinan jihar Jigawa
  • Alƙalin kotun ya umarci mataimakin sufeto janar na ƴan sanda (AIG) da ke shiyya ta ɗaya ya binciki zargin da ake yi wa Auwalu Danladi Sankara
  • Mai shari'a Ibrahim Yola ya ba da wannan umarnin ne bayan mijin matar ya shigar da ƙara a gaban kotun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wata kotun shari’ar Musulunci ta Kano ta umarci mataimakin sufeto janar na ƴan sanda (AIG) na shiyya ta ɗaya da ya binciki kwamishinan jihar Jigawa, Auwalu Danladi Sankara da aka dakatar.

Kotun ta umarci a binciki dakataccen kwamishinan ne bisa zargin yin lalata da wata matar aure, Tasleem Baba Nabegu.

Kara karanta wannan

NDLEA: Majalisa ta dauki mataki kan zargin kama kwayoyi a gidan sanata

Kotu ta umarci a binciki Auwalu Sankara
Kotu ta umarci 'yan sanda su binciki zargin da ake yi wa Auwalu Sankara Hoto: Auwalu D. Sankara, Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Alkalin kotun mai shari’a Ibrahim Yola ya bayar da wannan umarnin a ranar Talata, 22 ga watan Oktoban 2024, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sankara: Yadda zaman kotu ya kaya

Alƙalin ya ba da umarnin ne biyo bayan ƙarar da mijin Tasleem, Nasir Buba, ya shigar.

Ya buƙaci kotun musuluncin da ta umarci ƴan sanda su yi bincike kan alaƙar da ke tsakanin matarsa ​​da Sankara.

A zaman kotun na ranar Talata, lauyan waɗanda suka shigar da ƙara, Haruna Magashi, mai wakiltar Sa’id Muhammad Tudun Wada, ya shaidawa kotun cewa, suna da ƙwararan shaidu da ke tabbatar da zargin da suke yi wa mutanen biyu.

Ya ce shaidun sun haɗa da bidiyo, hotuna, hirar waya, musayar kuɗaɗe a tsakanin su, da sauran hujjoji.

Lauyan mata ya musanta zargi a kotu

A ɗaya ɓangaren kuma, lauyan Tasleem Baba Nabegu, Rabi’u Shuaibu Abdullahi, ya yi watsi da dukkan zarge-zargen da ake yi wa wanda yake karewa.

Kara karanta wannan

Taron NEC: Rikicin PDP ya ɗauki sabon salo, gwamna ya jagoranci kai ƙara kotu

Ya shaida wa kotun cewa an raba auren ma’auratan sama da shekara guda saboda cin zarafin da yake yi mata a lokacin da suke tare.

Hakazalika, lauyan Auwalu Danladi Sankara, Barista Aliyu Usman Hajji, ya bayyana zargin a ƙagen siyasa, da nufin bata sunan Sankara a matsayinsa na ɗan siyasa.

Wane hukunci alƙalin kotun ya yanke?

A hukuncin da ya yanke, mai shari’a Ibrahim Yola ya umurci AIG da ke Kano, da ya binciki lamarin sosai ba tare da tsangwama ko kama kowa ba.

Sannan ya miƙa karar zuwa wata babbar kotun jiha domin yin tuhuma.

Hisbah na neman kwamishina ruwa a jallo

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Hisbah ta Kano ta ayyana neman dakataccen kwamishinan ayyuka na musamman na Jigawa, Auwal Danladi Sankara ruwa a jallo.

Hukumar Hisbah ta fara neman kwamishinan ruwa a jallo ne bayan ya ƙi amsa gayyatar zaman sulhu da aka masa kan zargin lalata da matar aure.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng