Daga Karshe, Abba Ya Magantu kan Karin Albashi, Ya yi wa Ma'aikatan Kano Albishir

Daga Karshe, Abba Ya Magantu kan Karin Albashi, Ya yi wa Ma'aikatan Kano Albishir

  • Bayan kafa kwamiti, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya karbi rahoto kan maganar karin albashin ma'aikata a faɗin jihar
  • A yammacin yau Talata shugaban kwamitin karin albashi, Usman Bala ya bayyana abubuwan da suka lura da su yayin aikin
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana lokacin da gwamnatinsa za ta fadi mafi ƙarancin albashi da za ta cigaba da biyan ma'aikata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Abba Kabir Yusuf ya karbi rahoton kwamitin da ya kafa domin karin albashin ma'aikatan gwamnati.

Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa yana da tabbas a kan kwamitin zai yi aiki yadda ya kamata domin daidaita lamura.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya nada kawun Gwamna Abba Kabir Yusuf babban matsayi a masarautar Kano

Abba Kabir
Abba ya saka lokacin fadin mafi karancin albashi. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya wallafa yadda aka mika rahoton a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An mika rahoton karin albashi a Kano

Shugaban kwamitin karin albashi a jihar Kano, Bala Usman ya mika rahoto bayan sun kammala aiki.

A yammacin yau Talata, 22 ga watan Oktoba kwamitin ya mika rahoto ga Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatin jihar Kano.

Yadda kwamitin albashi ya yi aiki a Kano

Wanda ya jagoranci kwamitin, Bala Usman ya bayyana cewa sun yi dubi ga tattalin arzikin Kano a yayin aikin.

Usman ya kara da cewa sun yi adalci wa bangaren ma'aikata wajen ganin abin da za a biya su zai wadace su gudanar da rayuwar yau da kullum.

Yaushe Abba zai sanar da ƙarin albashi?

Abba Kabir Yusuf ya bukaci al'umma su kara hakuri wajen ba gwamnati lokaci ta yi nazari kan rahoton kwamitin.

Kara karanta wannan

Kano: Ana so a raba shi da Kwankwaso, Gwamna Abba ya amince da ayyukan N36bn

Gwamnan ya bayyana cewa a mako mai zuwa zai sanar da kudin da gwamnatinsa za ta rika biya a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Daliban Kano sun dawo daga Indiya

A wani rahoton, kun ji cewa a yammacin ranar Litinin tawagar gwamnatin Kano ta tarbi dalibai 29 da suka kammala karatu a Indiya.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin sama wa dukkan daliban aiki a jihar Kano bayan sun samu nasarar kammala digiri na biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng