Gwamnonin Arewa 2 Sun Sa Labule da Minista domin Kawo Karshen Rashin Tsaro

Gwamnonin Arewa 2 Sun Sa Labule da Minista domin Kawo Karshen Rashin Tsaro

  • Gwamnan jihar Zamfara da na Katsina sun ziyarci babban birnin tarayya, Abuja inda su ka gana da shugabannin tsaro
  • Gwamnonin biyu sun gana da Ministan tsaro, Muhammad Badaru da mashawarcin Bola Tinubu, Nuhu Ribadu
  • Hadimin gwamnan Katsina, Isah Miqdad ya ce an tattauna batutuwa tsaro domin inganta zaman lafiya a jihohin biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Matsalolin tsaron Arewacin kasar nan, musamman a jihohin Katsina da Zamfara sun sa an yi ganawa ta musamman a Abuja.

Wadanda su ka halarci taron sun hada da gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara, Dikko Umaru Radda na Katsina da karamin Ministan tsaro Muhammad Badaru.

Kara karanta wannan

Gwamna Dikko ya kere gwamnoni, an ba shi lambar yabo ta kasa da kasa a Faransa

Tsaro
Gwamnonin Zamfara da Katsina sun gana da jagororin tsaro a Abuja Hoto: @Miqdad_Jnr
Asali: Twitter

A sakon da hadimin gwamna Dikko Radda na jihar Katsina, Isah Miqdad ya wallafa a shafinsa na X, jagororin sun tattauna matsalar rashin tsaro a jihohin biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun yi tattaunawar sirri da Ministan tsaron kasar nan, Muhammad Badaru kan matsalolin da su ka addabi Katsina da Zamfara.

Tsaro: Gwamnoni sun gana da NSA

Gwamna Dauda Lawal Dare da takwaransa na jihar Katsina, Dikko Umaru Radda sun ziyarci mashawarcin Tinubu kan tsaro, Nuhu Ribadu.

A sakon da hadimin gwamnan Katsina, Isah Miqdad ya wallafa a shafin Facebook,ya ce wannan wani mataki ne na lalubo hanyar magance matsalar tsaro.

Dalilin ganawar gwamnoni da jagororin tsaro

Matsalar rashin tsaro da ta yi kamari a Arewa maso Yammacin kasar nan ya fi ta'azzara a jihohin Katsina da Zamfara da ke makwabtaka da juna.

Kara karanta wannan

Yadda Kwankwaso, Peter Obi, Abba da jiga jigan NNPP suka hadu yayin tarbar dalibai

An gudanar da ganawar sirri daban daban a ranar Talata, inda ake fatan haka zai zama daya daga hanyoyin kawo karshen rashin tsaro a jihohin.

Rundunar tsaro ta gargadi yan bindiga

A baya mun ruwaito cewa rundunar tsaron kasar nan ta ja kunnen masu garkuwa da mutane da sauran yan bindiga da su gaggauta dawo wa hayyacinsu.

Rundunar ta yi barazana ga dukkanin yan bindiga da su ka ki zubar da makamansu tare da mika wuya ga hukumomin tsaro cewa sojoji za su hallaka su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.