Gwamna a Arewa Ya Karya Tarihin Shekara 20, Ya Ƙarawa Ƴan Fansho Alawus Duk Wata

Gwamna a Arewa Ya Karya Tarihin Shekara 20, Ya Ƙarawa Ƴan Fansho Alawus Duk Wata

  • Gwamna Ahmed Usman Ododo na Kogi ya amince da ƙarin alawus na N10,000 ga dukkan masu karɓan fansho a jihar
  • Gwamna Ododo ya karya tarihin shekaru 20 da aka yi ba tare da waiwayar halin da ƴan fansho ke ciki ba a jihar da ke Arewa ta Tsakiya
  • Da yake jawabi, Gwamna Ododo ya ce gwamnatinsa za ta ɗora daga wurin da tsohon gwamna Yahaya Bello ya tsaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Gwamnan Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo ya amince da biyan N10,000 a matsayin alawus ga dukkan ƴan fansho a jihar.

Ahmed Ododo ya ɗauki wannan mataki ne bayan karɓar rahoto daga shugaban ma'aikatan jihar Kogi, Mr Elijah Evenemi a fadar gwamnatinsa da ke Lokoja.

Kara karanta wannan

Gwamna Dikko ya kere gwamnoni, an ba shi lambar yabo ta kasa da kasa a Faransa

Gwamna Ododo tare da ƴan fansho.
Gwamna Ododo ya kafa tarihi, ya amince da ƙarin alawus na N10,000 ga ƴan fansho Hoto: @Ihima_Principal
Asali: Twitter

Ya jadada kudirin gwamnatinsa na fifita walwalar al'umma, inda ya yabawa ƴan fansho bisa shafe shekaru suna yiwa jihar Ƙogi hidima, rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Ododo ya ɗaukarwa ƴan fansho alƙawari

Gwamnan ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta ɗora ne daga wurin da uban gidansa, tsohon gwamna Yahaya Bello ya tsaya.

Ya ƙara da cewa duk ɗan fanshon da ke karɓar ƙasa da N50,000 a wata za a sa shi a tsarin knshorar lafiya a matakin jiha da kananan hukumomi, cewar Daily Post.

Gwamna Ododo ya bayyana cewa tun da ya hau kan madafun iko, ƴan fansho ba su sake samun tangarɗa wajen biyansu haƙƙokinsu ba a kowane ƙarshen wata.

Ƴan fansho sun yabawa gwamnan Kogi

Tun da farko, shugaban kungiyar ’yan fansho ta jihar, Mista Ohida Otaru ya yaba wa gwamnan bisa yadda ya ɗauki tsofaffin ma'aikata da muhimmanci.

Kara karanta wannan

Mutane sun shiga matsala yayin da ruwa ya mamaye garuruwa 25, an samu bayanai

Mista Otaru ya ce shekaru 20 kenan ba a waiwayi halin da ƴan fansho ke ciki ba sai da Gwamna Ahmed Ododo ya zo.

Ya yabawa gwamnan musamman kan yadda ya ƙara kudin fansho da ake ba ma'aikatan da suka yi ritaya, wanda ya ce zai taimaka matuka wajen inganta rayuwarsu.

APC ta lashe zaɓen Kogi

A wani rahoton kuma hukumar zaben jihar Kogi (KSIEC) ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi 21 da aka gudanar ranar Asabar.

Hukumar ta tabbatar da cewa jam'iyyar APC mai mulkin jihar ta lashe dukan kujerun ƙananan hukumomi da kuma kansiloli 239 da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262