Gwamnatin Tarayya Ta Fadi Matsayarta kan Sulhu da 'Yan Bindiga

Gwamnatin Tarayya Ta Fadi Matsayarta kan Sulhu da 'Yan Bindiga

  • Gwamnatin tarayya Najeriya ta bakin ministan tsaro ta nesanta kanta da tattaunawa da ƴan bindiga masu kai hare-hare a ƙasar nan
  • Mohammed Badaru ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta yi sulhu da ƴan bindiga ba a halin da ake ciki a yanzu
  • Ministan tsaron ya ƙara da cewa za a ci gaba da kai hare-haren kan ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane har sai an fatattake su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ministan tsaro, Mohammed Badaru, ya bayyana matsayar gwamnatin tarayya kan tattaunawa da ƴan bindiga.

Mohammed Badaru ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba za ta yi sulhu da ƴan bindiga ba.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fadi lokacin kawo karshen rikicin manoma da makiyaya

Gwamnatin tarayya ba za ta yi sulhu da 'yan bindiga ba
Gwamnatin tarayya ta nesanta kanta da yin sulhu da 'yan bindiga Hoto: Mohammed Badaru
Asali: Facebook

Gwamnati ba za yi sulhu da ƴan bindiga ba

Ministan tsaron ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da jaridar Tribune lokacin da yaje duba dakarun sojojin Najeriya a Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohammed Badaru ya bayyana cewa yaje Kaduna ne duba sojojin bisa umarnin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Za a ci gaba da fatattakar ƴan bindiga

Ya kuma bayyana cewa za a ci gaba da yaki da ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane a yankin Arewa maso Yamma da sauran sassan ƙasar nan har sai an fatattake su.

"Ba za mu shiga tattaunawa ba. Za mu duba amfanin hakan da rashin amfaninsa. Amma a yadda abubuwa suke a yanzu, ba za mu tattauna da ƴan bindiga ba."
"Za ku yarda da ni cewa ana samun nasara kan hare-haren da sojoji suke kai wa ƴan bindiga. Don haka, shugaban ƙasa ya bukace ni da na zo na godewa sojojin saboda ƙwarewarsu da jajircewarsu wajen gudanar da ayyukansu."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace babban jami'in gwamnati da mutane masu yawa a Zamfara

- Mohammed Badaru

Minista ya magantu kan sulhu da ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi magana kan sulhun da ya yi da ƴan bindiga a lokacin da yake gwamnan Zamfara.

Bello Matawalle wanda tsohon gwamnan jihar Zamfara ne ya kare matakin da ya ɗauka na yin sulhu da ƴan bindigan a lokacin gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng