Bayan Jefa Arewa a Duhu, Gwamnati Ta Fara Binciken Matsalar Wutar Lantarki

Bayan Jefa Arewa a Duhu, Gwamnati Ta Fara Binciken Matsalar Wutar Lantarki

  • Gwamnatin tarayya ta damu kan matsalar lalacewar turakun lantarki da ake fama da shi a sassan kasar nan, musamman yankin Arewa
  • Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya jagoranci kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan dalilan lalacewar wutar lantarki
  • Ministan ya yi takaici matuka kan yadda yawan lalacewar wutar lantarki zai shafi ci gaban da gwamnatin Tinubu ta samu a bangaren

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Yawaitar matsalar wutar lantarki da ake samu ya kasar nan ya jawo hankalin gwamnatin tarayya wajen gano matsalar.

Ministan makamashi na kasa, Adebayo Adelabu da shugabannin hukumar rarraba hasken lantarki na kasa (TCN) da na hukumar kula da wutar lantarki na kasa (NERC) sun yi ganawar sirri.

Kara karanta wannan

TCN ta bayyana abin da ya jawo lalacewar wutar lantarki a Arewacin Najeriya

Bola Tinubu
An kafa kwamitin duba matsalar lantarki Hoto: Bola Tinubu Ambassadors
Asali: Facebook

Tashar TVC News ta wallafa cewa Adebayo Adelabu ya bayyana rashin jin dadi kan yadda turakun lantarkin kasar nan ke yawaita lalacewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lalacewar lantarki: Wane matakin aka dauka?

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Ministan makamashi na kasa ya kafa kwamitin mutum shida da zai yi duba kan matsalar lantarkin kasar.

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Bolaji Tunji, inda ake sa ran kwamitin zai gano inda matsalar ta ke.

Minista ya koka kan matsalar lantarki

Ministan makamashin Najeriya, ya ce yawaitar katsewar turakun lantarkin kasar nan zai kawo nakasu kan nasarar da gwamnatin Tinubu ta samu a bangaren.

Ministan ta bakin hadiminsa, Bolaji Tunji ya bayyana cewa gwamnati ta yi nasarar samun karuwar megawatts 5,527 na lantarki tun bayan hawanta mulki.

Kara karanta wannan

Yaushe za a dawo da wutar lantarki a Arewacin Najeriya? TCN ya yi bayani

An fadi dalilin lalacewar turakun lantarki

A wani labarin kun ji cewa kamfanin rarraba hasken lantarki na TCN ya bayar da rahoto kan dalilin lalacewar wutar a sassa daban daban na Arewacin Najeriya.

Manajan hulda da jama’a na kamfanin TCN, Ndidi Mbah da ya yi bayanin, ya kara da cewa layukan wuta a tashar Ugwaji-Apir ne ya fadi, ya kuma jawo gagarumar matsala a rarraba wutar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.