Mafi Karancin Albashi: Ana Murna, Gwamna Ya Sanar da Lokacin Fara Biyan N70,000
- Gwamnatin Abia ta sanar da lokacin da za ta fara biyan ma'aikatanta sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 da aka amince da shi a ƙasar nan
- Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alex Otti ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashin ga ma'aikata a cikin watan Oktoban 2024
- Kwamishinan yaɗa labaran jihar wanda ya sanar da hakan ya yi nuni da cewa gwamnatin za ta iya yi wa ma'aikata ƙari kan N70,000 a wata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Abia - Gwamnatin jihar Abia ta bayyana matsayarta kan fara biyan ma'aikata mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Gwamnatin ta bayyana cewa za ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoban 2024.
Gwamnatin Abia za ta biya albashin N70,000
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Abia, Prince Okey Kanu ya bayyana hakan a ranar Talata yayin ganawa da manema labarai, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta biyo bayan taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a ranar Litinin, wanda Gwamna Alex Otti ya jagoranta.
Okey Kanu ya ce matakin ya ƙara jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na inganta jin daɗin ma’aikata, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Akwai yiwuwar ma'aikata su samu ƙari
Ya kuma yi nuni da cewa yayin da N70,000 shi ne mafi ƙarancin albashin da ake yanke a ƙasar nan, a shirye gwamnatin jihar take ta yi ƙari idan buƙatar hakan ta taso.
"Gwamnati jiha ta amince da mafi ƙarancin albashi, sannan a cikin ƴan kwanaki kaɗan masu zuwa za a fara biyan albashin."
"Idan har gwamna yana son ya biya abin da yafi wanda aka amince da shi a matakin ƙasa, hakan zai faru."
- Prince Okey Kanu
Gwamnan Abia ya ba matasa shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya ba matasan Najeriya shawara kan su shiga cikin harkokin siyasa.
Gwamna Alex Otti ya buƙaci matasan Najeriya da su shiga harkokin siyasa domin yanke shawara kan makomarsu da kuma kawo sauyi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng