Barayi Sun Tasa Abuja a gaba, Majalisa Ta Gayyato Ministan Tinubu da DSS

Barayi Sun Tasa Abuja a gaba, Majalisa Ta Gayyato Ministan Tinubu da DSS

  • Majalisar wakilan Najeriya ta bayyana takaicin yadda ake samun karuwar garkuwa da mutane a birnin tarayya Abuja
  • Wannan ya biyo bayan kudurin da dan majalisa, Isma'il Dabo ya gabatar kan yawaitar sace jama'a a babban birnin
  • Majalisar ta bukaci jagororin rundunar yan sanda, DSS da Ministan Abuja su gaggauta bayyana a gabanta kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta gaji da yawaitar garkuwa da mutane da miyagun yan ta'adda ke yi a babbar birnin tarayya Abuja a kwanakin nan.

Lamarin ya sa dan majalisa, Isma'il Dabo ya gabatar da kudurin gaggawa a gaban majalisar a zamanta na ranar Talata, 22 Oktoba, 2024.

Kara karanta wannan

"Sun zama maboyar miyagu:" FCTA ta bayar da wa'adin kammala gine gine a Abuja

Nyesom
Majalisa ta gayyaci Ministan Abuja, DSS kan rashin tsaro Hoto: Nyesom Ezenwo Wike/The Nigerian Senate
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa majalisar ta dauki matakin binciko yadda lamarin satar jama'a ke kamari a babban birnin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Satar Mutane: Majalisa ta gayyaci Ministan Abuja

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci Ministan Abuja, Nyesom Wike ya gaggauta bayyana a gabanta domin bayani kan karuwar satar mutane birnin.

A kwanakin nan ne wasu bata gari suka kashe daya daga cikin hadiman dan majalisar, Isma'il Dabo bayan sun yi mata sata.

Majalisa ta nemi DSS saboda satar mutane

Majalisar wakilai ta nemi jagororin hukumomin tsaron kasar nan su bayyana a majalisa domin a samu bayanan abin da ke faruwa kan garkuwa da jama'a.

Majalisar ta bukaci kwamishinan yan sanda, Peter Opara da daraktan DSS, Adeola Ajayi da su zo domin yi mata bayanin halin da ake ciki.

Za a rushe gine-gine a birnin Abuja

Kara karanta wannan

Obasanjo ya fadi kokarin da ya yi da yake mulki, ya koka da rashin tsaro a yau

A baya mun ruwaito cewa hukumar gudanarwar babban birnin tarayya Abuja na shirin rushe wasu daga cikin gine-ginen da ke Abuja biyo bayan fargabar sun zama matattarar bata-gari.

Hukumar FCTA ce ta fadi haka, inda ta ba masu gine-ginen da ba a karasa ba wa'adin watanni uku domin kammala su ko kuma hukumar Abuja ta ruguza su domin kare rayukan jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.