Gwamna Ya yi Barazanar Sauke Sarakuna saboda Rashin Tsaro
- Gwamnatin jihar Taraba ta gargadi sarakunan gargajiya kan tashin hankali da ake yawan samu a yankunan da suke mulki
- Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Muhammad Alkali ne ya wakilci gwamna Agbu Kefas a wani taron samar da zaman lafiya
- Legit ta tattauna da wani mazaunin Karim Lamido, Muhammad Abubakar Rahama domin jin yadda ake rikicin kabilanci a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Taraba - Gwamantin jihar Taraba ta yi kira na musamman ga sarakunan gargajiya kan muhimmacin samar da zaman lafiya.
Agbu Kefas wanda ya samu wakilci ya ce gwamnati za ta dauki mataki mai tsauri a kan duk wani sarki da aka samu da hannu kan rashin tsaro.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa gwamnatin Taraba ta yi gargaɗin ne yayin wani taron zaman lafiya a karamar hukumar Karim Lamido.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya yi barazana ga sarakunan Taraba
Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya yi barazanar sauke duk wani sarki da aka samu da hannu kan matsalar tsaro.
Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdullahi Alkali ya ce daga yanzu gwamnati ba za ta lamunci tayar da rikici ba a kowane yanki.
An yi rikici tsakanin Fulani da Gommu
An samu rikici tsakanin yan ƙabilar Fulani da Gommu a karamar hukumar Karim Lamido inda aka rasa rayuka.
Gwamna Agbu Kefas ya ce ran shi ya ɓaci matuka kan lamarin kuma sanadiyyar haka ne ma ya dauki matakin tura mataimakinsa garin.
Sarakuna sun yi magana a Taraba
Sarkin kauyen Bikwin, Bitrus Bala Sarkin Yara ya bayyana cewa za su cigaba da ƙoƙarin samar da zaman lafiya a jihar Taraba.
Shugaban kungiyar Tabbital Fulani, Ardo Njarenga Galdo ya ce dole a rika jan hankulan matasa idan ana son samun zaman lafiya a jihar.
Legit ta tattaunda Muhammad Abubakar
Wani mazaunin Karim Lamido, Muhammad Abubakar Rahama ya zantawa Legit cewa ana yawan samun rikicin kabilanci a yankin.
Muhammad ya ce matakin barazanar sauke sarakuna da gwamnati ta dauka zai saka shugabanin kokarin taka birki ga matasa masu tayar da fitina.
An kama masu taimakon yan bindiga
A wani rahoton, kun ji cewa an kama mata da miji cikin wadanda ake zargi da adana makamai da yan bindiga a jihar Taraba.
Rahotanni sun nuna cewa an kama mata da mijin ne a karamar hukumar Lau ta jihar tare da wani mutum da suke ta'adi tare.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng