Tuna baya: Hotunan sarakuna 7 da aka taba tube wa rawani
Tube rawanin Malam Muhammadu Sanusi II da Gwamna Ganduje yayi a ranar Litinin ya ci gaba da jawo cece-kuce. Wasu na cewa ana tsammanin hakan za ta faru amma wasu har yanzu suna cikin tsananin mamaki. Wasu kuwa cewa suka yi ba a taba yi wa Sarkin babbar masarauta irin ta Kano makamancin haka ba. Wasu kuwa cewa suka yi hakan ba za ta iya faruwa ba a wasu sassan kasar nan.
Amma kuma, ba tun yau ba aka saba tube rawunan sarakuna ba ko masu mulki. Daya daga cikin makamantan hakan ya faru ne a kalla shekaru 100 da suka gabata.
Ga wasu manyan sarakuna da suka taba fuskantar makamancin abinda Malam Muhammadu Sanusi II ya fuskanta.
1. Adeyemi Adeniran II ya hau karagar mulkin masarautar Oyo ne a 1945 kuma ya sauka daga karagar ne bayan shekaru 10. Shugaban yankin yamma na lokacin, Obafemi Awolowo ya saukesa saboda dalilan siyasa.
2. Adesoji Aderemi ya bar mulkin masarautar Ife ne bayan ya kwashe shekaru 50 a kan karagar. Shine basaraken farko na masarautar da ya iya karatu da rubutu kuma mai tarin dukiya ne. Ya yi gwamnan yankin yammaci a tsakanin 1960 zuwa 1962 kafin marigayi Ladoke Akintola ya saukesa.
3. An tube rawanin tsohon sarki Musulmi Ibrahim Dasuki ne a ranar 20 ga watan Afirilu 1996, shekaru 8 bayan hawansa karagar.
Tsohon shugaban kasar mullkin soji, Sani Abacha ne ya bada wannan umarnin. An mayar da shi Yola inda daga baya ya koma Jalingo da ke jihar Taraba don samun mafaka. Daya daga cikin abinda yasa aka yi hakan kamar yadda gwamnatin lokacin ta sanar, shine saka kiyayya a tsakanin mutane da kuma gidan sarautar. Hakazalika, akwai rashin biyayya ga umarnin gwamnati.
DUBA WANNAN: Tube rawanin Sanusi: Dattijan Kano sun yi wa Ganduje zazzafan martani
4. Bayan fada da gwamnatin turawa a wancan lokacin, an saukesa ne sakamakon kashe wani babban jami’i mai suna James Philips da aka yi yayin da ya kai ziyara masarautar a 1897.
Hukumomin sun kama basaraken sannan aka gurfanar da shi gaban kotu inda aka kama shi da laifi. Daga nan kuwa ne aka tube masa rawaninsa.
5. Wa ke tuna Sarki Oluwadare Adesina wanda shine deji na Akure da ke jihar Ondo? Basaraken yayi fada da matarsa ne a cikin bainar jama’a wanda hakan yasa aka tube masa rawaninsa a 2009. Gwamnatin jihar Ondo din ta dogara da sashi na 17 sakin layi na daya da na biyu ne na dokokin sarautar jihar. An koresa daga Akure na watanni shida yayin da matarsa wacce a yanzu ta rasu, ta maka shi kotu.
6. A watan Yuni na 2005, gwamnatin jihar kebbi ta tube rawanin Mustapha Jokolo wanda shine sarkin Gwandu na 19 sakamakon zarginsa da tayi da yin maganar da za ta kawo kalubale ga tsaron kasa. Ya tattara da iyalansa ya koma jihar Kaduna amma daga bisani wata babbar kotun jihar Kebbi din ta bukaci ya koma kujerarsa.
7. Umaru Tukur ya hau karagar masarautar Muri a 1966 kuma shine sarki na 11. Bayan shekaru 20 da hawa karagar mulkin, ya samu matsala da Yohana Madaki, gwamnan jihar Gongola na wancan lokacin. A ranar 12 ga watan Augustan 1986 ne gwamnan ya bada umarnin tube rawanin Tukur tare da bada umarnin korarsa zuwa Mubi da ke jihar Adamawa ta yanzu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng