'Yan Bindiga Sun Tare Babbar Hanya, Sun Kashe Matafiya, An Sace Wasu da Dama

'Yan Bindiga Sun Tare Babbar Hanya, Sun Kashe Matafiya, An Sace Wasu da Dama

  • Gungun 'yan bindiga sun tare babbar hanyar Tsafe zuwa Funtua da ke a jihar Zamfara, suka kashe fasinjoji kuma aka sace wasu
  • An ce 'yan bindigar sun kaddamar da harin ne a yammacin ranar Litinin, kuma sun bude wuta lokacin da suka ci karo da motocin
  • Wani mazunin yankin ya ce jami'an tsaro sun isa wurin da aka kai harin, an ce sun bi bayan 'yan bindigar amma basu hadu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - 'Yan bindiga sun kashe matafiya da dama tare da yin garkuwa da wasu a kan hanyar Tsafe zuwa Funtua da ke jihar Zamfara.

Majiya sun bayyana cewa lamarin ya faru da misalin karfe 6 na yammacin Litinin a daidai kauyen Kucheri da ke a karamar hukumar Tsafe.

Kara karanta wannan

Jigawa: Adadin wadanda suka mutu a fashewar tanka ya haura 175, bayanai sun fito

'Yan bindiga sun farmaki matafiya a kan hanyar Tsafe zuwa Funtua, an kashe mutane da dama
Zamfara: 'Yan bindiga sun kashe mutane da dama a hanyar Tsafe zuwa Funtua.
Asali: Original

'Yan bindiga sun kashe matafiya a Zamfara

Wani mazaunin garin, wanda ya zanta da jaridar Daily Trust ya bayyana yadda ‘yan bindigar suka tare motoci a kan titin da ke da ya saba ganin cunkoson ababen hawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mazauna garin ya ce ‘yan bindigar sun bude wuta a kan titin, lamarin da ya tilasta motoci tsayawa, nan take suka kashe wasu fasinjoji tare da yin awon gaba da wasu.

"Sun kashe wasu fasinjoji tare da sace wasu," a cewar mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa.

Jami'an tsaro sun kai dauki bayan harin

Wani mazaunin garin, Musa Yusuf ya tabbatar da cewa jami’an tsaro da suka hada da DSS, ‘yan sanda da kuma jami’an CPG sun isa wurin jim kadan bayan harin, inji SaharaReporters.

Ya ce jami’an tsaron sun jajanta wa wadanda suka tsira daga harin tare da bin sawun ‘yan bindigar, duk da cewa daga baya sun dawo ba tare da kwato wadanda aka sace ba.

Kara karanta wannan

Zaune bata kare ba: Tsageru sun ci gaba da ta'addanci a Arewa, sun tafka barna a Katsina

A baya-bayan nan dai hanyar Tsafe-Funtua ta zama wurin da ‘yan bindiga ke kai yawan hare-hare, duk da cewa akwai shingayen tsaro da dama a kan hanyar.

Kokarin jin ta bakin kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara CP Muhammad Shehu Dalijan domin jin ta bakinsa ya ci tura.

'Yan bindiga sun sace jami'in gwamnatin Zamfara

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun sace shugaban hukumar tattara kuɗin shiga da kasafi (RMAFC) na jihar Zamfara, Bashir Abara Gummi.

Bayanai sun nuna cewa 'yan bindigar sun yi garkuwa da Alhaji Bashir ne tare da wasu mutane masu yawa a hanyar Funtua zuwa Gusau.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.