Kotun Koli Ta Dauki Mataki kan Karar da Ke Neman Rusa Hukumar EFCC
- Kotun Koli ta tanadi hukunci kan ƙarar da gwamnoni 16 suka shigar inda suke ƙalubalantar dokar da ta kafa EFCC
- Kotun mai alƙalai bakwai ta tanadi hukunci ne kan ƙarar yayin zamanta na ranar Talata, 22 ga watan Oktoban 2024
- Wasu daga cikin jihohin da ke cikin ƙarar sun sanar da janyewarsu daga shari'ar inda kuma kotun ta amince da hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kotun Ƙoli ta ɗauki mataki kan ƙarar da ke ƙalubalantar dokar da ta kafa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC).
Kotun Ƙolin a zamanta na ranar Talata, 22 ga watan Oktoban 2024 ta tanadi hukunci a ƙarar wacce jihohi 16 na Najeriya suka shigar.
EFCC: Yaushe kotun kolin za ta yi hukunci?
Kotun mai alƙalai bakwai ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Uwani Abba-Aji ta tanadi hukuncin ne a ranar Talata, 22 ga watan Oktoban 2024, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta tanadi hukuncin ne bayan ta kammala sauraran bayanai daga bakin lauyoyin da ke cikin shari'ar, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Kotun ta sanar da ɓangarorin da ke cikin shari'ar cewa za ta sanar musu da ranar da za a yanke hukunci.
Gwamnoni sun shigar da hukumar EFCC ƙara
Ƙarar da tun da farko Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na jihar Kogi ya shigar, ta samu wasu jihohin da suka shiga a matsayin masu shigar da ƙara.
Jihohin da suka shiga cikin ƙarar mai lamba SC/CV/178/2023 sun haɗa da Ondo, Edo, Oyo, Ogun, Nasarawa, Kebbi da Katsina.
Sauran jihohin su ne: Sokoto, Jigawa, Enugu, Benue, Anambra, Plateau, Cross-River da Neja.
Hakazalika, Antoni Janar na jihohin Anambra, Adamawa da Ebonyi sun sanar da janyewarsu daga ƙarar, kotun ta amince da hakan.
Yadda EFCC ta ƙwato N200bn
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ta kwato sama da N200bn a cikin shekara ɗaya.
EFCC ta kuma samu nasarar sanyawa kotuna su yankewa mutane kusan 3,000 hukunci a shekara ɗaya a ƙarƙashin jagorancin Ola Olukoyede.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng