TCN Ta Bayyana Abin da Ya Jawo Lalacewar Wutar Lantarki a Arewacin Najeriya

TCN Ta Bayyana Abin da Ya Jawo Lalacewar Wutar Lantarki a Arewacin Najeriya

  • Kamfanin TCN ya bayar da rahoton lalacewar wutar lantarki a Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya
  • Manajan hulda da jama’a na TCN, Ndidi Mbah ya bayyana cewa wasu layukan wuta da ke kan tashar Ugwaji-Apir ne suka samu matsala
  • Bayan faruwar hakan, kamfanin TCN ya bayyana cewa an aike da tawagar masu aikin gyaran layin wuta domin shawo kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin wutar lantarkin Najeriya (TCN) ya ce layukan samar da wuta na 1 da na 2 masu karfin 330kV da ke Ugwaji-Apir a Arewa sun samu matsala.

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da kamfanin TCN ya sanar da cewa babbar tashar wutar lantarki ta lalace karo na uku a cikin mako guda.

Kara karanta wannan

Gyaran tattalin arziki: Manyan nasarori 5 da gwamnatin Tinubu ta samu a 2024

Kamfanin TCN ya yi magana kan lalacewar wutar lantarki a Arewacin Najeriya
Kamfanin TCN ya bayyana cewa wutar lantarki a Arewa ta samu matsala amma ana gyara. Hoto: Prapat Aowsakorn
Asali: Getty Images

An dauke wuta a Arewacin Najeriya

A cewar TCN, wannan matsalar da aka samu ce ta jawo daukewar wutar lantarki a jihohin Arewacin Najeriya a halin yanzu, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban manajan hulda da jama’a na kamfanin TCN, Ndidi Mbah ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata.

Sanarwar Ndidi Mbah ta ce:

"Matsalar da aka samu ta tilasta dauke wutar lantarki a garuruwan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da kuma sassan Arewa ta Tsakiya."

Matsalar da wuta ta samu a jihohin Arewa

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“Da misalin karfe 4:53 na safe, layi na 2 da ke kan tashar Ugwuaji–Markurdi ya samu matsala inda aka mayar da karfin megawatt 243 a kan layi na 1.
"Da karfe 4:58 na safe, Layi na 1 shi ma ya samu tangarda, wanda ya haifar da asarar megawatt 468 gaba daya.

Kara karanta wannan

Yaushe za a dawo da wutar lantarki a Arewacin Najeriya? TCN ya yi bayani

"Da misalin karfe 5:15 da 5:17 na safe aka sake gwada amfani da layin 1 da layi na 2, amma duka suka samu matsala a lokaci guda."

Rahoton Punch ya nuna cewa bayan faruwar lamarin, kamfanin na TCN ya ce an aika da tawagogin masu aikin gyaran layin wuta domin shawo kan lamarin.

Najeriya na kai wa makwabta wutar awa 24

A wani labarin, mun ruwaito cewa duk da matsalar wuta da ake samu, Najeriya na ba kasashen Togo, Nijar da Benin wutar lantarki ta sa'o'i 24.

Shugaban kamfanin TCN, Sule Abdulaziz wanda ya bayyana hakan, ya ce kasashen na biyan kudin wutar da suka sha don haka suke samun wutar babu daukewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.