Kaduna: Masarautar Zazzau Ta Ƙara Yin Babban Rashi, Wani Ɗan Sarki Ya Rasu
- Sarkin Dawakin Tsakar Gida na masarautar Zazzau, Alhaji Ibrahim Shehu Idris ya riga mu gidan gaskiya a karshen makon da ya gabata
- Alhaji Ibrahim, ɗan marigayi sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya rasu ne yana da shekaru 47 a duniya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
- A wata sanarwa da masarautar Zazzau ta fitar, ta ce an yi wa marigayi sallar Jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Masarautar Zazzau da ke jihar Kaduna ta ƙara yin rashin wani yarima karo na biyu a wata guda, Alhaji Ibrahim Shehu Idris ya riga mu gidan gaskiya.
Wannan rashi dai na zuwa ne kwanaki 21 bayan rasuwar Ɗan Isan Zazzau, Alhaji Umar Shehu Idris.
Alhaji Ibrahim Shehu Idris, ɗan marigayi sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya rasu ne yana da shekaru 47 a duniya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masarautar Zazzau ta kara rasa yarima
Marigayin shi ke riƙe da sarautar Sarkin Dawakin Tsakar Gida na masarautar Zazzau da ke jihar Kaduna a Arewa maso Yammacin Najeriya.
Bayanai sun nuna cewa Alhaji Ibrahim ya rasu ya bar iyali da suka haɗa da mata da ƴaƴa huɗu.
Mai magana da yawun masarautar Zazzau, Abdullahi Aliyu Kwarbai, ya tabbatar da rasuwar marigayin a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce marigayin ya rasu ne a yammacin Lahadin da ta gabata a asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Shika, Zariya.
An yi masa sallar Jana'iza a fadar sarki
Abdullahi Aliyu Kwarbai ya kara da cewa Alhaji Ibrahim ya koma ga Allah ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
"An gudanar da sallar jana'izar marigayi Sarkin Dawakin Tsakar Gida a fadar mai martaba Sarkin Zazzau a Zariya da misalin karfe 11 na safiyar ranar Litinin," in ji sanarwar.
Masarautar Zazzau ta dakatar da Hakimi
A wani rahoton kun ji masarautar Zazzau da ke jihar Kaduna ta dakatar da wani Hakimi bisa zargin daukar mataki da hannunsa na cin zarafi.
An dakatar da Marafan Yamman Zazzau, Alhaji Mustapha Adamu Ubaidullah saboda zargin ya sa an bugi wani matashi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng