Obasanjo Ya Fadi Tsohon Shugaban Kasa 1 da Ya Ke Kishi da Shi, Ya Fadi Dalilansa

Obasanjo Ya Fadi Tsohon Shugaban Kasa 1 da Ya Ke Kishi da Shi, Ya Fadi Dalilansa

  • Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya kira sunan Janar Yakubu Gowon musamman, ya yaba masa
  • Obasanjo ya ce yana kishi da Janar Gowon saboda yadda ake yabonsa tun bai mutu ba bayan shugabancin Najeriya
  • Tsohon shugaban kasar ya kwatanta Janar Gowon da tsohon Firaministan Birtaniya, Winston Churchill

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yaba da rayuwar Janar Yakubu Gowon.

Tsohon shugaban kasar ya ce Gowon yana matukar burge shi duba da yadda ake yabonsa tun yana raye.

Obasanjo ya yabawa tsohon shugaban kasa, Janar Gowon
Olusegun Obasanjo ya yabawa Janar Yakubu Gowon saboda yadda ake yabonsa. Hoto: Goodluck Jonathan/@TeslakiddT.
Asali: UGC

Obasanjo ya yabawa tsohon shugaban kasa, Gowon

Punch ta ce Obasanjo ya fadi haka ne yayin wani babban taro a birnin Abuja a jiya Litinin 21 ga watan Oktoban 2024.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya fadi kokarin da ya yi da yake mulki, ya koka da rashin tsaro a yau

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obasanjo ya ce Gowon na daya daga cikin tsofaffin shugabannin Najeriya da ya ke kishi da su, Vanguard ta ruwaito.

Tsohon shugaban kasar ya ce a kullum yana kwatanta Gowon da tsohon Firaministan Birtaniya, Winston Churchill.

Ya ce suna da kaman-ceceniya duba da yanayin gudunmawar da suka bayar a kasashensu.

"Shugabanni ƙalilan ne ake yabonsu a rayuwarsu, Janar Gowon ina kishi da kai saboda ana yabonka tun kana raye."
"Ka kasance kamar Winston Churchill, saboda ba kowane shugaba ba ne ake yabonsa kamar yadda ake maka, wannan iko ne na Ubangiji."

- Olusegun Obasanjo

Karanta karin labarai da suka shafi Gowon

Kara karanta wannan

'Ta dawo makabarta': Obasanjo ya fadi dalilin rashin samun cigaba a Najeriya

Obasanjo ya soki shugabannin Najeriya

Mun ba ku labarin cewa, tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya caccaki tsarin shugabancin Najeriya.

Obasanjo ya ce akwai tsare-tsare masu kyau a kasar amma an rasa masu aiwatar da su domin kawo sauyi a Najeriya baki ɗaya.

Tsohon shugaban kasar ya ce abin takaici ne yadda ake watsi da tsare-tsare masu kyau saboda rashin kishin kasa da zagon kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.