Shari'ar N100bn: Dangote Ya Canza Mataki kan Karar Gwamnati da Ya Shigar

Shari'ar N100bn: Dangote Ya Canza Mataki kan Karar Gwamnati da Ya Shigar

  • Rukunin kamfanonin Dangote ya yi magana kan karar da ya shigar a babbar kotun tarayya na hana NNPCL da 'yan kasuwa shigo da mai
  • A ranar 6 ga Satumbar 2024 ne Dangote ya shigar da hukumar NMDPRA kara gaban kotun kan ba kamfanonin lasisin shigo da mai
  • Sai dai a sanarwar da kamfanin Dangote ya fitar ranar Litinin, ya ce a yanzu babu bukatar ci gaba da shari'ar don haka zai janye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A wani al’amari mai ban mamaki, kamfanin Dangote ya ce zai janye karar Naira biliyan 100 da ya shigar da Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA).

Kara karanta wannan

An barke da murna da kamfanin NNPCL da Chevron suka sake hako wata rijiyar mai

Dangote ya shigar da karar ne saboda NMDPRA ya ba kamfanin NNPCL, Matrix Petroleum Services, AA Rano Limited da wasu kamfanoni hudu lasisin shigo da mai.

Dangote ya yi magana kan karar da shigar da hukumar NMDPRA a kotu
Dangote ya ce zai janye karar N100bn da ya shigar da gwamnati. Hoto: @nnpclimited
Asali: Twitter

Rukunin kamfanonin Dangote ya bayyana shirinsa na janye wannan karar ne a daren ranar Litinin, 21 ga Oktoba kamar yadda rahoton Channels TV ya nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote zai janye karar da ya shigar

A cikin sanarwar, Dangote ya ce karar da ya shigar a babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar 6 ga Satumba, 2024, “tsohon batu ne” kuma al’amura sun rinjayi karar.

Wani mai magana da yawun kamfanin, Anthony Chiejina ya ce bangarorin da lamarin ya shafa sun fara tattaunawar sulhu.

The Punch ta rahoto Anthony Chiejina ya kuma ce matatar man ba ta da niyyar ci gaba da wannan shari’ar.

“Mun amince da dakatar da shari’ar. Ya na da kyau mu sanar da cewa karar ba ta yi wata illa ga kowane bangare ba."

Kara karanta wannan

'Rashin darajar Naira ka iya zama alheri', CBN ya fadi yadda za a inganta Najeriya

- A cewar Anthony.

Menene ya kai Dangote shigar da kara?

A karar da ya shigar, Dangote ya bayar da hujjar cewa NMDRA ta take sashe na 317(8) da (9) na dokar masana’antar man fetur (PIA) ta hanyar ba da lasisin shigo da mai alhalin babu karancin man a kasar.

Matatar Dangote ta yi iƙirarin cewa irin waɗannan lasisin ana bayar da shi ne kawai a lokutan da ake da buƙatar shigo da wani samfurin mai.

Kamfanin ya bayyana cewa lasisin shigo da man da aka bai wa wasu kamfanoni na da illa ga matatarsa, wanda ya kashe biliyoyin daloli wajen ganin ya fara aiki.

IPMAN ta gaza samun man Dangote

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan kasuwar man Najeriya karkashin kungiyar IPMAN sun bayyana cewa har yanzu ba su iya samun man fetur daga matatar Dangote ba.

Shugaban kungiyar IPMAN, Abubakar Maigandi ya ce a halin yanzu 'yan kasuwa ba su da tabba kan jigilar fetur duk da an fara tace shi a gida Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.