NDLEA: Sanata Ya Yi Kakkausan Martani kan Zargin Kama Kwayoyi a Gidansa
- Sanatan da ke rigima da NDLEA, Oyelola Ashiru ya karyata zargin da hukumar ke yi masa na ta'ammali da miyagun kwayoyi
- A sanarwar da hadimin Sanatan, Olaitan Adeyanju ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa NDLEA na yi masa kazafi ne kawai
- Shugaban hukumar NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ne ya ce an kama kwayoyi a gidan Sanatan da ke Kwara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Kwara ta Kudu, Oyelola Yisa Ashiru ya zargi hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) da yi masa kazafi.
Sanatan ya fadi haka ne ta cikin sanarwar da hadiminsa, Olaitan Adeyanju ya fitar a ranar Litinin a matsayin martani kan zargin da NDLEA ta yi masa.
Jaridar The Cable ta wallafa cewa hukumar NDLEA ta bayyana gano wasu miyagun kwayoyi a gidan Sanatan bayan jami'anta sun kai sumame.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"NDLEA ta yi karya:" Sanata Ashiru
Jaridar The Nation ta tattaro cewa Sanatan da NDLEA ke zargi an kama kwayoyi a gidansa ya musanta cewa shi ya dauki hadiman da aka ce an gano.
A sanarwar da hadimin Sanata Oyelola Yisa Ashiru ya fitar, ya bayyana cewa babu masu sunan Ibrahim Mohammd da Mohammed Yahaya a cikin hadiman Sanatan.
Sanata ya nemi NDLEA ta tafi kotu
Sanatan Kwara ya shawarci hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi da ta gaggauta kai wadanda ta ce an kama a gidansa a gaban kotu idan da gaske ne.
Sanata Oyelolo Ashiru ya ce tabbas jami'an NDLEA sun binciki gidansa da ke Kwara, kuma ba a samu wani abin laifi ba kamar yadda hukumar ke ikirari.
"Mun kama kwaya a gidan Sanata:" NDLEA
A baya mun wallafa cewa shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaa ya ce an kama miyagun kwayoyi a gidan Sanata Oyelola Ashiru.
Wannan na zuwa bayan Sanata Ashiru a nemi majalisar dattawa ta amince a ruguje hukumar biyo bayan samun lam'a kan yadda ta ke gudanar da ayyukanta na yaki da safarar kwaya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng