Rundunar Tsaro Ta Gargadi Yan Bindiga, Sojoji Sun ba Su Zabi 2

Rundunar Tsaro Ta Gargadi Yan Bindiga, Sojoji Sun ba Su Zabi 2

  • Rundunar tsaron kasar nan ta gargadi yan bindiga da sauran yan ta'addan da su ka addabi Arewa da cewa karshensu ya zo
  • Shugaban rundunar Fansar Yamma, Janar Oluyinka Soyele ya yi gargadin bayan kai ziyara ga gwamna Dauda Lawal a Zamfara
  • Ya ba yan bindiga zabi guda biyu, inda ya ce su na iya mika wuya ko kuma zaratan sojojin kasar nan su aika su lahira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Rundunar sojin kasar nan ta jaddada matsayarta na kai farmaki har maboyar yan ta'addan da su ka addabi jama'a, musamman a Arewacin kasar nan.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun kashe shugabannin yan ta'adda bayan fafatawa

Shugaban rundunar Fansar Yamma, Manjo Janar Oluyinka Soyele ne ya yi gargadin jim kadan bayan ganawarsa da gwamna Dauda Lawal a fadar gidan gwamnatin Zamfara.

Zamfara
Rundunar tsaro ta nemi yan ta'adda su mika wuya ko a kashe su Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

AIT ta tattaro cewa Manjo Janar Oluyinka Soyele ya kore shakku kan yakin da su ke yi da ta'addanci, inda ya tabbatar da cewa za su yi maganin yan bindiga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ku mika wuya:" Sojoji ga yan bindiga

Rundunar sojojin kasar nan ta ba yan ta'adda shawarar su mika wuya ga hukumomin kasar nan ko jami'an tsaro su hallaka su har lahira.

Shugaban rundunar Fansar Yamma, Manjo Janar Oluyinka Soyele da ya yi gargadin a Zamfara ya kuma sha alwashin cewa dakarunsu za su kwato mutanen da aka yi garkuwa da su.

Sojoji sun nemi hadin kan jama'a

Manjo Janar Oluyinka Soyele ya nemi hadin kan jama'ar kasar nan, domin ta haka ne za a iya kakkabe ayyukan ta'addanci.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bani: Sojoji za su samu jiragen yaki 50 domin zafafa luguden wuta

Shugaban dakarun Fansar Yamma ya kara bayar da tabbacin dawo da zaman lafiya jihar, musamman bayan karuwar ayyukan yan ta'adda a kwanakin nan.

An fara sakin fursunoni bayan kama yan bindiga

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Zamfara ta fara sakin daurarrun da ke gidan ajiya da gyaran hali a jihar biyo bayan karuwar kama yan bindiga da jami'an tsaro ke yi.

A ziyarar da gwamna Dauda Lawal ya kai gidan gyaran hali da ke Gusau, ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnati ta kara sanya idanu kan gidan kurkuku saboda karuwar kama yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.