'Ku Yi Masu Addu'a Kawai': Uwargidan Tinubu Ta Gargadi Malamai kan Zagin Masu Mulki

'Ku Yi Masu Addu'a Kawai': Uwargidan Tinubu Ta Gargadi Malamai kan Zagin Masu Mulki

  • Uwargidan shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gargadi malaman Najeriya da na kasashen Afrika da su kauracewa zagin shugabanni
  • Sanata Remi Tinubu ta ce malamai sun koma tsinewa masu rike da madafun iko maimakon su yi masu addu'a da nasihar jan hankali
  • Shugaban kungiyar CAN, Daniel Okoh ya bayyana damuwa kan kalubalan da ake fuskanta a kasar nan musamman na tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu ta gargadi malamai kan zagi da aibata masu madafun iko.

Sanata Oluremi Tinubu ta ce kamata ya yi a ce malamai su mayar da hankali kan yin addu'o'i da nasiha ga masu mulki maimakon a yi musu ruwan tsinuwa.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Uwargidan Shugaba Bola Tinubu ta yi magana kan yadda malamai ke zagin masu mulki.
Uwargidan shugaban kasa ta gargadi malamai kan zagin masu rike da madafun iko. Hoto: @SenRemiTinubu
Asali: Facebook

Uwargidan shugaban kasar ta yi wannan gargadin ne a wajen bikin bude taron kungiyar African Biblical Leadership Initiative a Abuja, inji rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ka da ku zagi shugananni" - Remi Tinubu

Taron kungiyar ABLI na da taken, "tsarin shugabancin Afrika da ya jawo hankalin shugabannin kirista na kasashen Afrika da Turai."

Uwargidan Tinubu ta bukaci shugabannin addinai da su yi wa’azin zaman lafiya kuma su bi sawun Yesu Almasihu ta wajen yin addu’a ga masu madafun iko maimakon cin zarafinsu.

Remi Tinubu ta ce:

“Ga iyayenmu na ruhaniya, ina rokonku da ku samar da zaman lafiya da ci gaba tare da yi wa gwamnati addu’a.
"Ka da mu tsine ko mu zagi gwamnati. Ku rika fadawa shugabanni gaskiya."

An ce Remi Tinubu ta samu wakilcin kodineta ta kasa kuma babbar jami'ar cibiyar bunkasa Afrika ta NPAD, Princess Gloria Akobundu.

Kara karanta wannan

Jita jitar rashin lafiyar Tinubu da abubuwan da suka faru bayan tafiyarsa hutu

CAN ta yi korafi kan tsadar rayuwa

Tun da farko, shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya, Daniel Okoh, ya yi kakkausar suka kan bukatar da ke da akwai na samar da shugabanci na gari.

Okoh ta kuma yi addu’ar Ubangiji ya ci gaba da samar da shugabanni masu kishin kasa da tausayin al'ummar kasashen Afirka.

"Muna fuskantar ƙalubale masu yawa, kamar rashin tabbas na tattalin arziki, rashin adalci na zamantakewa da rikice-rikice da ke barazana ga haɗin kai da ci gabanmu.

- Shugaban CAN

'Lokacin da talaka zai samu sauki' - Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa uwargidan shugaba Bola Tinubu ta ce ba mijin ta ne ya jefa 'yan Najeriya a tsadar rayuwar da suke ciki ba.

Matar shugaban kasar ta ba 'yan Najeriya tabbacin cewa nan da shekaru biyu masu zuwa Najeriya za ta samu gagarumin ci gaba mai dorewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.