Jami'ai Sun Kama Kwayoyi a Gidan Sanatan da Yake So a Rusa Hukumar NDLEA

Jami'ai Sun Kama Kwayoyi a Gidan Sanatan da Yake So a Rusa Hukumar NDLEA

  • Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta zargi Sanata mai wakiltar Kwara ta Kudu da hada-hadar miyagun kwayoyi
  • Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ne ya yi zargin ta cikin sanarwar da kakakin hukumar, Femi Babafemi ya fitar
  • Janar Buba Marwa mai ritaya ya bayyana cewa jami'an NDLEA sun samu wasu miyagun kwayoyi a gidan Sanata Oyeyola Ashiru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kwara - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta bayyana dalilin da Sanata mai wakiltar Kwara ta Kudu, Oyeyola Ashiru ke neman a rufe ta.

Kara karanta wannan

Rigimar APC ta sake dagulewa da Sanata Wamakko da Lamido suka ja ɓangarensu

A zaman majalisar dattawan kasar nan na ranar 15 Oktoba, 2024, Sanata Oyeyola Ashiru ya nemi majalisar ta sa baki a ruguje hukumar NDLEA.

NDLEA
NDLEA ta zargi Sanata da cinikin miyagun kwayoyi Hoto: NDLEA
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta tattaro a cewar Sanata Ashiru, hukumar NDLEA na cike da rashawa, inda ya kara da shaidawa yan majalisa cewa akwai shakku a cikin yadda ta ke gudanar da ayyukanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar NDLEA ta yi martini ga Sanata

Jaridar The Cable ta wallafa cewa shugaban NDLEA na kasa, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya caccaki kudurin Sanata Ashiru na neman a ruguje hukumar.

Shugaban NDLEA ya bayyana cewa jami’an hukumar sun kama miyagun kwayoyi a gidan dan majalisar da ke wakiltar Kwara ta Kudu.

“Ba mu da tsoro” -;NDLEA ga Sanata Ashiru

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta bayyana cewa Sanata Oyeyola Ashiru ba zai firgita su ba duk da kokarin jawo masu matsala da ya ke yi.

Kara karanta wannan

Yadda ‘yan siyasar jihar Kano 4 suka zagaya kujera 1 cikin shekaru 8 a gwamnatin tarayya

Shugaban hukumar ta bakin jami’in hulda da jama’arta, Femi Babafemi ya jaddada matsayarsu na lalata duk wasu wurare da ake hada-hadar kwayoyi, har da na gidan Sanatan.

NDLEA za ta yi wa dalibai gwaji

A baya mun wallafa cewa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta ce akwai shirin da ta ke yi na gwada daliban kasar nan domin gano masu ta'ammali da miyagun kwayoyi.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Femi Babafemi ya bayyana cewa an bullo da shirin ne domin gano daliban da ke bukatar taimako wajen rabuwa da matsalar shaye-shaye a makarantu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.