COAS: DHQ Ta Bayyana Gaskiya kan Batun Nada Mukaddashin Hafsan Sojin Kasa

COAS: DHQ Ta Bayyana Gaskiya kan Batun Nada Mukaddashin Hafsan Sojin Kasa

  • Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta musanta rahotannin da ke yawo kan cewa ta naɗa muƙaddashin hafsan sojin ƙasa
  • DHQ ta buƙaci masu yaɗa jita-jita kan lafiyar hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagabaja da su daina yin hakan
  • Muƙaddashin daraktan yaɗa labarai na DHQ ya bayyana cewa Lagbaja ya tafi hutu ne kuma zai dawo ba da jimawa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro ta (DHQ) ta yi magana kan batun naɗa muƙaddashin hafsan sojojin Najeriya (COAS).

DHQ ta sanar da cewa ba ta naɗa wanda zai zama COAS yayin da Taoreed Lagbaja ya tafi hutu ba.

DHQ ta musanta nada mukaddashin COAS
DHQ ta ce Taoreed Lagbaja na cikin koshin lafiya Hoto: Headquarters Nigerian Army
Asali: Facebook

DHQ ta musanta naɗa muƙaddashin hafsun soji

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da muƙaddashin daraktan yaɗa labarai na tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya fitar a ranar Litinin a shafin X na DHQ.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi wa ƴan Najeriya albashir da ASUU ke shirin rufe jami'o'i

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tukur Gusau ya ce babu irin wannan naɗin a cikin rundunar sojojin Najeriya, yana mai cewa babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya yi magana da Taoreed Lagbaja ƴan mintuna kaɗan da suka gabata.

A cewarsa, hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, a halin yanzu ya tafi hutu ne.

Ya bayyana cewa ana tafiyar da rundunonin sojoji cikin ƙwarewa, ya ƙara da cewa dukkanin hafsoshin tsaro na gudanar da ayyukansu kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tanada.

Birgediya Janar Tukur Gusau ya fayyace cewa Manjo Janar Abdulsalam Ibrahim, wanda shi ne shugaban sashen tsare-tsare, ya na ba da bayanai ga Lagbaja kan ayyukan rundunar na yau da kullum.

DHQ ta yi wa jama'a gargaɗi

"DHQ ta buƙaci mutanen da ke yaɗa jita-jita marasa tushe da su daina yin hakan nan take.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ministan Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya su daina korafi, ya ba su shawara

"COAS yana cikin ƙoshin lafiya kuma nan ba da jimawa ba zai dawo bakin aiki bayan ya kammala hutunsa."

- Birgediya Janar Tukur Gusau

Kakakin na DHQ ya gargaɗi masu kiran sojoji su ƙwace mulki su sani cewa irin waɗannan ayyukan cin amanar ƙasa ne a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin ƙasar nan.

Rundunar sojoji ta magantu kan batun rasuwar Lagbaja

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Nigeriya ta yi martani kan jita-jitar rasuwar hafsan sojoji, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja.

Rundunar ta musanta rade-radin da ake yi cewa Lagbaja ya riga mu gidan gaskiya a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, 20 ga watan Oktoban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng